Jaridar Hasken Rana

  • Home
  • Jaridar Hasken Rana

Jaridar Hasken Rana Online Media News
(1)

ALLAH SARKI AREWADAVIDO YAYI AMFANI DA DAMAR DA YA SAMU...a lokachin da rarara ya kwashe kusan rabin yan social media da...
12/06/2026

ALLAH SARKI AREWA

DAVIDO YAYI AMFANI DA DAMAR DA YA SAMU...

a lokachin da rarara ya kwashe kusan rabin yan social media da yan tiktok da wasu daga cikin yan film da mawaka ya kai su abuja domin neman sake yiwa yan siyasa campaign

Shi kuma DAVIDO yayi amfani da damar da ya samu ta FIFA World Cup 2026 Countdown Concert a a birnin los angeles

Ya nunawa duniya halin da al'ummar Nigeria musamman jihar oyo suke cikin

Ya rubuta a bayan rigarsa BRING THEM HOME sannan ya rubuta sunayen duk daliban da aka sace da malamansu a jikin rigar sa

Wannan babbar dama ce wacce duniya zata san meya faru don a yanzu haka wannan abun da yayi ya jawo hankalin duk wani babba a Nigeria kuma kasashen duniya hankalinsu ya kai ga matsalat satar daliban da akayi da malaman da akayi a jihar oyo

Yak**ata duk dan Arewa a yaɗa wannan saƙon domin mutane su sani

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKILYau barayin daji sun farmaki garin Gora Namaye dake karamar hukumar Maradun jihar Zamfara, ...
12/06/2026

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL

Yau barayin daji sun farmaki garin Gora Namaye dake karamar hukumar Maradun jihar Zamfara, sun sa|wantar da ra¥ukan mutane kusan 20

Kuma barayin sun k**a mutane da yawa sun tafi dasu daji, an gudanar da Sallah Jana'iza na wadanda har¡n ya rutsa da su

Don Allah masu iko da tsaron Kasarnan ku sake dabarun yaki, yaki da matsalar nan ba da karfin Soji bane, ku sake lissafi, ba zai yiwu a cigaba da tafiya a haka ba gaskiya

Allah Ka jikan wadanda aka ka$he, Allah Ka yaye mana ba don halayen mu ba

Nanda Shekara 100 Mai Zuwa Adamawa Bazata taba Mantawa da GWAMNA FINTIRI ba. Daga Auwal Usman Fintiri 1. Biya kudin Waec...
12/06/2026

Nanda Shekara 100 Mai Zuwa Adamawa Bazata taba Mantawa da GWAMNA FINTIRI ba.

Daga Auwal Usman Fintiri

1. Biya kudin Waec/Neco, Uniform kyauta, Karatun karatu, da kayan rubutu kyauta ga yaran Talakawa.

2. Fintiri za a rinka tunawa dashi a ko da yaushe bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen Bada Tallafi Na Kayan Sana'oi Da Tallafi na Kudi ga Tallakawa misali PAWECA da Sauran Su.

3. Za a rinka tunawa da Fintiri a matsayin Gwamna wanda ya tabbatar da cewa an gyara dukkan makarantun firamare da na gaba da firamare a jihar.

4. Za a ci gaba da tunawa da Fintiri a matsayin Gwamna Mai Hawa 2 wanda ya yi nasarar daukar Tallakawa Fiye 20,000 da s**a kammala karatu a ma'aikatan jihar.

5. Za a rinka tunawa Fintiri a matsayin Gwamnan da ya sayi sabbin motocin bas masu kujeru 58 da kuma Luxurious guda 10 domin saukaka matsalolin sufuri a jihar.

6. Wasu daga cikin cigaban ababen more rayuwa da gwamnatin Gov Fintiri ta yi a jihar Adamawa za a dade ana tunawa da su a tarihin jihar Adamawa. Gwamnati Fintiri ce farko da ta yi gadar sama guda 5 kasa da shekaru 7 kacal.

7. Za a tuna da Fintiri a matsayin Gwamnan da ya gina Asibitocin Cottage guda 8 a Fadin Jihar.

Don Allah a gaya wa Makiya waɗancan asibitocin an gina su ne domin rage rashin aikin yi a tsakanin matasa a Jihar Adamawa.

8. Fintiri za a rinka tunawa dashi a matsayin Gwamna wanda ya bada Tallafi karatun Kyauta wa daliban da s**a yi fice a matakin digiri na farko Zuwa na gaba.

9. Za a rinka tunawa da Fintiri a matsayin Gwamna wanda ya tabbatar da cewa Talakawa sun kwana a gidajensu ta hanyar samar da tsaro a duk fadin Kanana hukumomi Guda 21 da Muke Dasu a fadin jihar.

10. Fintiri za a rinka tunawa dashi a matsayin Gwamnan da ya gina sabuwa kasuwa ta shopping complex, Wajen Taro International Conferences Center, Wajen Kallon Kafa Stadium, Sabuwa Gidan Ajiyar Namu Daji, (Zoo) Sabuwa Kasuwa Na Yola South Da Manya Manya Wajen Koyan Sana'a Ga Tallakawa Jihar.

11. Haka kuma za a tuna da alawus dinsa na Dubu 30 kyauta ga ‘yan bautar kasa (NYSC) da suke hidima a jihar Adamawa

12. A Gwamnatin Fintiri an biya albashi, da fansho akan lokaci. idan aka kwatanta da Gwamnatin baya.

13. Gwamnatin Fintiri ta gyara da gina sabbin makarantun sakandire da s**a hada da Model Secondary Schools, sannan ta saka hannun jari a kwalejin fasaha, kirkire-kirkire da nazarin harkokin kasuwanci ta jihar Adamawa Gulak Madagali. Akan kiwon lafiya, Asibitin Uwa da Yara na Yola Ya inganta manyan asibitoci.

Marubuci: ✍️ Auwal Usman Fintiri
Hadimi Na Musamma Ga Gwamna Jihar Adamawa.

An K**a Matasa Yayin Ƙoƙarin Sace Transformer a Garin Tsamaye, Sabon Birni — SokotoAn k**a wasu matasa da ake zargin sun...
12/06/2026

An K**a Matasa Yayin Ƙoƙarin Sace Transformer a Garin Tsamaye, Sabon Birni — Sokoto

An k**a wasu matasa da ake zargin suna ƙoƙarin sace na’urar wutar lantarki (transformer) a garin Tsamaye da ke cikin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa an cafke matasan ne a lokacin da suke kokarin kwance tare da tura transformer ɗin domin sace shi, kafin a kai ga nasarar kammala aikinsu.

Lamarin ya jawo hankalin mazauna yankin, inda daga bisani aka mika su ga hukumomin da s**a dace domin gudanar da bincike da daukar mataki.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawan samun korafe-korafe kan satar kayan wutar lantarki a wasu sassan jihar.

RUNDUNAR ’YAN SANDAN ADAMAWA TA KARYATA SAƘON DA KE YAWO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA GAME DA WASU ƊAUKE DA MAKAMAI A BAGALE ...
12/06/2026

RUNDUNAR ’YAN SANDAN ADAMAWA TA KARYATA SAƘON DA KE YAWO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA GAME DA WASU ƊAUKE DA MAKAMAI A BAGALE HOTEL, JIMETA

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa tana sanar da jama’a cewa wani hoto da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ke nuna wasu mutane ɗauke da mak**ai tare da taken "Bagale Hotel, Jimeta", ba gaskiya ba ne.

Saboda haka, Rundunar tana kira ga jama’a da su yi watsi da wannan saƙo tare da gujewa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da ingancinsu ba, waɗanda ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro. Rundunar na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar, tare da ƙarfafa wa jama’a gwiwa da su riƙa dogaro da sahihan hanyoyin samun bayanan tsaro.

Haka kuma, Rundunar tana gargaɗin masu yaɗa ƙarya da bayanan da ba su da tushe cewa duk wanda aka samu da hannu a irin wannan aiki zai fuskanci hukunci daidai da tanadin doka.

SP Suleiman Yahaya Nguroje,
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda
Madadin Kwamishinan ’Yan Sanda
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa

12 ga Yuni, 2026.

“Mahaifina na ɗaya daga cikin shugabannin Najeriya da aka fi rashin fahimta a tarihin ƙasar nan, amma a gare ni mutum ne...
12/06/2026

“Mahaifina na ɗaya daga cikin shugabannin Najeriya da aka fi rashin fahimta a tarihin ƙasar nan, amma a gare ni mutum ne nagari kuma mai kishin Najeriya.”

— Zainab Sani Abacha, diyar tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Janar Sani Abacha.

Ta bayyana cewa mahaifinta ya taka muhimmiyar rawa wajen tara wasu kuɗaɗen ajiyar ƙasa domin kare Najeriya daga matsalolin tattalin arziƙi a nan gaba.

A cewarta:

"Da ace mahaifina mutum ne mai son alatu da nuna isa, da ya kashe waɗannan kuɗaɗe wajen sayen jiragen ruwa masu tsada, jiragen sama na kansa, ko gina manyan kadarori a ƙasashen waje. Amma bai yi hakan ba, domin yana kallon makomar Najeriya ne."

Ta ƙara da cewa tana da yaƙinin cewa wata rana ‘yan Najeriya za su sake nazarin tarihin mahaifinta cikin adalci, su fahimci irin rawar da ya taka da kuma manufarsa ga ƙasar.

“Na yi imani wata rana gaskiya za ta bayyana, kuma ‘yan Najeriya za su fahimci ko wanene Sani Abacha a zahiri.”

Menene ra'ayinku kan wannan furuci na Zainab Abacha?

Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar a ranar Alhamis, yiwuwar "rattaɓa hannu" kan yarjejeniya da Iran a ƙarshen wannan...
12/06/2026

Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar a ranar Alhamis, yiwuwar "rattaɓa hannu" kan yarjejeniya da Iran a ƙarshen wannan mako...

Fiye Da 'Yan Bindiga 13,000 Muka Kawar A Cikin Shekara Ɗaya – Shugaba TinubuTinubu ya bayyana hakan ne a wani ɓangare na...
12/06/2026

Fiye Da 'Yan Bindiga 13,000 Muka Kawar A Cikin Shekara Ɗaya – Shugaba Tinubu

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani ɓangare na jawabinsa na ranar Dimokuraɗiyya, inda ya ce hukumomin tsaro sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan da s**a addabi wasu sassan ƙasar.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa jami'an tsaro da kayan aiki da dabarun zamani domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a faɗin Najeriya.

Tinubu Ya Bai Wa ’Yan Bindiga Wa’adi Su Miƙa WuyaShugaba Bola Tinubu ya gargaɗi ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ...
12/06/2026

Tinubu Ya Bai Wa ’Yan Bindiga Wa’adi Su Miƙa Wuya

Shugaba Bola Tinubu ya gargaɗi ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da su miƙa wuya ko su fuskanci hukuncin gwamnati.

A jawabinsa na ranar Dimokuraɗiyya, ya ce gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da ɗaukar sabbin jami’an tsaro da ware Naira tiriliyan 5.41 a kasafin 2026 domin tsaro. Tinubu ya ce kofar sulhu tana buɗe ga masu miƙa wuya, amma ya jaddada cewa ba za ta kasance a buɗe har abada ba.

Kalla yanda ak**a wani barawo kifi a jihar benuwe.
12/06/2026

Kalla yanda ak**a wani barawo kifi a jihar benuwe.

Address

Wuse 2 Abuja

Telephone

+2348189217438

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Hasken Rana posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share