07/10/2025
Zargin Tarkardun Bogi: ministan kere-kere da kimiyya da fasaha yayi murabus
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din ministan kere-kere da kimiyya da fasaha Geoffrey Uche Nnaji, biyo bayan wasu zarge-zarge da ake masa.
Shugaba Tinubu ya nada Nnaji a watan Agusta 2023 a matsayin minitsan. Ya yi murabus ne a yau a wata wasika inda ya gode wa shugaban kasar da ya ba shi damar yi wa Najeriya hidima.
Nnaji ya ce abokan hamayyar siyasa sun yi masa zagon kasa