Ragaya Hausa Nigeria

Ragaya Hausa Nigeria An Bude Wannan Shafi Na Ragaya Hausa Nigeria 20/03/26 Don Samar Da Sahihan Labarai Da Dumi~Duminsu Na Gida Da Ketare.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran gargaɗi cewa za ta fuskanci hare-hare mafi muni idan ta yi yunƙurin kashe shi...
11/07/2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran gargaɗi cewa za ta fuskanci hare-hare mafi muni idan ta yi yunƙurin kashe shi, yana mai cewa sojojin Amurka sun shirya tsaf domin mayar da martani cikin ƙarfi.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, Trump ya ce:

“Mak**an roka dubu ɗaya a shirye suke su afka wa Iran idan ta aiwatar da duk wata barazana ta kashe ni, nan take za a harba ƙarin dubban mak**ai masu linzami.”

Trump ya kuma ce ya bayar da umarnin da s**a dace, yana mai cewa sojojin Amurka sun shirya su “lalata dukkan yankunan Iran gaba ɗaya” na tsawon shekara guda.

Wannan barazanar na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an leƙen asirin Isra’ila sun gano wani sabon shiri da ake zargin Iran na yi na kashe Trump.

Haka kuma, an ga wasu hotuna da kalamai masu nuna adawa da Trump a yayin jana’izar Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Sai dai jami’an Iran sun sha musanta zarge-zargen cewa suna da wani shiri na kashe Donald Trump.

‘Yan sandan jihohi za su kawo tsaro kusa ga ‘yan Nijeriya - IGP Tunji DisuSifeto janar na ’yan sandan Nijeriya, Tunji Di...
11/07/2026

‘Yan sandan jihohi za su kawo tsaro kusa ga ‘yan Nijeriya - IGP Tunji Disu

Sifeto janar na ’yan sandan Nijeriya, Tunji Disu ya ce, kafa rundunar ’yan sandan jihohi za ta ƙarfafa tsaron al’umma tare da inganta tattara bayanan sirri, saboda jami’an za su fi sanin mutanen yankunan da suke aiki.

Sai dai ya ce har yanzu ana kan matakin shirye-shirye, inda za a gudanar da tattaunawa, nazari da koyon darasi daga ƙasashen da ke aiwatar da tsarin kafin a fara aiki da shi gaba ɗaya.

Gwamnatin Kebbi ta rufe makarantu a yankunan da ƴan bindiga s**a addabaGwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa makarantun ...
09/07/2026

Gwamnatin Kebbi ta rufe makarantu a yankunan da ƴan bindiga s**a addaba

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa makarantun da aka rufe a al'ummomin da matsalar 'yan bindiga ta shafa za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai tsaro ya inganta.

Gwamnatin ta ce matakin da aka ɗauka kimanin watanni bakwai da s**a gabata ya samo asali ne ta la'akari da rashin tsaro, inda za a sake buɗe makarantun a lokacin da aka tabbatar da lafiyar ɗalibai da malamai.

Sojoji sun yi ajalin ƴan bindiga takwas, sun dakile shirin kai hari kan matafiya a KatsinaDakarun Rundunar Sojin Najeriy...
09/07/2026

Sojoji sun yi ajalin ƴan bindiga takwas, sun dakile shirin kai hari kan matafiya a Katsina

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kashe wasu da ake zargin ƴan bindiga ne su takwas tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da babura guda biyar a wani samame da s**a kai a karamar hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.

Yanzu haka sojojin Nigeria sunyi nasarar kashe sama da yan bindiga 300 a garin Gummi dake jahar Zamfara.
09/07/2026

Yanzu haka sojojin Nigeria sunyi nasarar kashe sama da yan bindiga 300 a garin Gummi dake jahar Zamfara.

Mashigin Hormuz zai kasance a bude ne bisa sharudanmu - Gwamnatin IranIran ta sake jaddada cewa ita ce za ta tsara yadda...
09/07/2026

Mashigin Hormuz zai kasance a bude ne bisa sharudanmu - Gwamnatin Iran

Iran ta sake jaddada cewa ita ce za ta tsara yadda ake zirga-zirga ta Mashigin Hormuz, tana mai zargin Amurka da karya yarjejeniyar zaman lafiya da kasashen biyu s**a rattaba hannu a kanta bayan sabbin hare-haren da Washington ta kai wa kasar da ke yankin Gabas ta tsakiya.

Majalisar Dattawan Nijeriya za ta yi wani zama kan takaddamar kasafin kuɗin hukumar bogi a ranar TalataAna sa ran Majali...
06/07/2026

Majalisar Dattawan Nijeriya za ta yi wani zama kan takaddamar kasafin kuɗin hukumar bogi a ranar Talata

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tattauna kan cece-kucen da s**a biyo bayan ware hukumar da ake zargi da kasancewa bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council, kuɗi har naira biliyan 1.3 a cikin Kasafin Kuɗi na shekarar 2026, yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Jaridar The PUNCH ta kuma gano cewa an karɓi wata wasiƙar naɗi ta bogi mai ɗauke da sa hannun jabu na Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a Hedikwatar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ba tare da cikakken tantancewa ba.

Hakan ya bai wa Prince Adeniyi Adeyemi Mathew damar samun ofishi a rukunin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja, lamarin da ya sa wannan hukuma mai cike da cece-kuce ta yi k**a da halastacciyar hukuma ta gwamnati na tsawon fiye da shekara guda.

An hana Jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei halartar jana'izar mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei saboda dalilai na t...
04/07/2026

An hana Jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei halartar jana'izar mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei saboda dalilai na tsaro, k**ar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta ruwaito.

Ta'azzarar yunwa a Arewacin Nijeriya abin damuwa ne matuka - Peter ObiDan takarar shugabancin Nijeriya na jam'iyyar NDC ...
04/07/2026

Ta'azzarar yunwa a Arewacin Nijeriya abin damuwa ne matuka - Peter Obi

Dan takarar shugabancin Nijeriya na jam'iyyar NDC a zaben 2027 Peter Obi ya nuna damuwa kan abin da ya ce ta'azzarar yunwa a yankin Arewacin Nijeriya.

Wannan ya biyo bayan wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 17 a jihohin Arewa 9 na fama da matsananciyar yunwa, k**ar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

An sace wa wata alƙaliya sama da Naira miliyan 7 - EFCCShugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana yadda wasu da ak...
04/07/2026

An sace wa wata alƙaliya sama da Naira miliyan 7 - EFCC

Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana yadda wasu da ake zargi da damfarar intanets**a kwashe sama da Naira miliyan 7.2 daga asusun wata alƙaliya mai aiki cikin dare guda.

Olukoyede ya ce kuɗin su ne ajiyar da alƙaliyar ta yi tsawon shekara shida domin biyan kuɗin karatun ɗanta.

Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wasu littattafai biyu da tsohuwar alƙaliyar babbar kotu, Mai Shari’a Alaba Omolaye-Ajileye, ta wallafa.

Address

ABUJA
Abuja
123456

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ragaya Hausa Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share