Muryar Hausa

Muryar Hausa muryar Hausa tashar labarai ce da Harshen Hausa zallah

ADC Marigayi Muhammadu Buhari Na Farko Jiya Yayi Aikinsa Na Karshe Ga Mai Gidansa Muhammadu BuhariSunansa Lt. Col. Muham...
16/07/2025

ADC Marigayi Muhammadu Buhari Na Farko Jiya Yayi Aikinsa Na Karshe Ga Mai Gidansa Muhammadu Buhari

Sunansa Lt. Col. Muhammad Lawan Abubukar Shine ADC Buhari Na Farko Daga 2015 Har Zuwa Zangon Mulkinsa Na Biyu a February 2022 Ya Tafi Kasar Waje Domin Course Din Samun Promotion Daga Col. Zuwa Bridge General Wanda Lt. Col. YM Dodo Ya Maye Gurbinsa Amatsayin Sabon Dogarin Buhari Ma'ana Sabon ADC.

Jiya Yayi Aikinsa Na Karshe Ga Mai Gidansa
Baba Allah Ya Kyautata Makwanci..🤲-🤲

📷 Rabiu Garba Gaya:

Tinubu ya umarci Shettima ya tafi London don rako gawar Buhari Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar tsohon...
13/07/2025

Tinubu ya umarci Shettima ya tafi London don rako gawar Buhari

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a birnin London da yammacin yau bayan fama da doguwar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa daga mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce Buhari ya rasu misalin karfe 4:30 na yamma ranar Lahadi, 13 ga watan Yuni, 2025.

Ya ce Tinubu ya tattauna da Hajiya Aisha Buhari, matar marigayin tsohon shugaban kasa, inda ya mika ta’aziyyarsa tare da jajanta mata bisa wannan babban rashi.

Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da ya tafi Birtaniya domin raka gawar marigayin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Najeriya.

Marigayin Buhari ya yi mulki sau biyu a matsayin zababben shugaban kasa tsakanin 2015 da 2023, sannan ya shugabanci kasar a matsayin shugaban soja daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985.

A matsayin girmamawa ga marigayin shugaban kasa, Shugaba Tinubu ya umarci a sauko da tutar Najeriya kasa.

Innalillahi wainna Ilaihi Rajiun!Allah Ya yi wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rasuwaMai magana da yawun tsohon ...
13/07/2025

Innalillahi wainna Ilaihi Rajiun!

Allah Ya yi wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rasuwa

Mai magana da yawun tsohon shugaban Garba Shehu ne ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce iyalin Buharin ne s**a sanar.

Allah ya jikansa da rahama

DA DUMI-DUMI: Nigeria zata ƙara kuɗin wutar lantarki, ana tsaka da rashin samun wutar a Nigeriar
09/07/2025

DA DUMI-DUMI: Nigeria zata ƙara kuɗin wutar lantarki, ana tsaka da rashin samun wutar a Nigeriar

Ba zan iya riƙe shugabancin gamayyar ƙungiyoyin ƴan kasuwa ta Kano ba - SKYShugaban kamfanin SKY Alhaji Kabiru Sani Kwan...
06/07/2025

Ba zan iya riƙe shugabancin gamayyar ƙungiyoyin ƴan kasuwa ta Kano ba - SKY

Shugaban kamfanin SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya ce ba zai iya rike mukamin Uban Gammayya kungiyoyin yan kasuwa na jihar Kano ba, wanda kungiyar ta nada shi makon da ya gabata bayan rasuwar Alhaji Aminu Dantata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da SKY ya sanyawa hannu da kansa kuma Mai magana da yawunsa Kamal Yakubu Ali ya aikewa manema labarai.

Ya ce mukamin da su ka ba shi Babban Mukami ne da ba zai iya dauka ba, don haka ya yanke shawarar sauka daga mukamin kwanaki uku bayan nada shi.

Yakasai ya ce “Jama’a muna kara godiya da duk ni’imar da Allah ya yi mana da kauna da ake nuna mana dare da rana da girmamawa da ake mana.

“Ina bada hakuri da fatan alheri ga gamaryar kungiyoyi yan kasuwar jihar Kano bisa nadi da s**a yimun na shugabancinsu a matsayin UBA NA KUNGIYA da su yi hakuri a kan wannan matsayin ya yi min nauyi bazan IYABA. Amma ina tare da su a duk al’amuransu musamman inda ake bukatar gudunmawata.

“Allahumma Salli Ala Sayyidanan Muhammad wa ala alihi” Ni Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ina mika ta aziyyar ga al’ummar Nigeria gaba daya bisa rasuwar babanmu Alhaji Aminu Alhassan Dantata da sauran mutanen da muka rasa baki daya mace da namiji, Allah ya gafartamusu amin.

06/07/2025

I got over 500 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

Jagororin APC a Jihar Kano sun ƙauracewa tarbar mataimakin shugaban KasaYayin da mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shetti...
03/07/2025

Jagororin APC a Jihar Kano sun ƙauracewa tarbar mataimakin shugaban Kasa

Yayin da mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya kawo ziyara Jihar Kano a wannan Rana domin ta'aziyyar rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata, ba'a hangi fuskokin jagororin Jam'iyyar APC na Jihar Kano a wajen tarbarsa, sabanin yadda ake gani a baya idan ya kawo ziyara Jihar Kano.

Ko me hakan yake nufi ?

Mutane uku da s**a rasu a wata kasa aka yi jana’izarsu a Masallacin Harami Madina. Tarihi ya nuna cewar waɗannan mutanen...
02/07/2025

Mutane uku da s**a rasu a wata kasa aka yi jana’izarsu a Masallacin Harami Madina.

Tarihi ya nuna cewar waɗannan mutanen su kaɗai ne s**a samu wannan dacen:

1. Muhammad Al-Badr – Shi ne Sarki na ƙarshe a ƙasar Yemen kafin juyin mulki ya kifar da mulkinsa. Ya rasu ne a birnin London a shekarar 1996.

2. Zine El Abidine Ben Ali – Tsohon shugaban ƙasar Tunisia wanda ya mulki ƙasar na tsawon lokaci kafin juyin juya hali. Ya rasu ne a birnin Jeddah, Saudiya, a shekarar 2019.

3. Alhaji Aminu Alhassan Dantata – Fitaccen ɗan kasuwa daga Kano, Najeriya. Ya rasu ne a birnin Abu Dhabi, Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), ranar Asabar 28 ga Yuli, 2025.

Dukkan waɗannan fitattun mutane, iyalan su sun nemi izinin gwamnatin Saudiyya domin gudanar da sallar jana’iza a cikin Masallacin Harami da ke birnin Madina mai alfarma — buƙatar da ba kasafai akan amince da ita a kowane lokaci ba.

Allah Ya jaddada masu rahama.

A wani abu mai ban sha'awa da Nasir El-Rufai jagoran SDP ya gabatar da kudurin neman a zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar haɗ...
02/07/2025

A wani abu mai ban sha'awa da Nasir El-Rufai jagoran SDP ya gabatar da kudurin neman a zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka, a inda Mr. Peter Obi jagoran Labour Party (LP) ya amince da kudurin El-Rufai wato (seconded).

A nan take aka zaɓi Sanata David Mark a matsayin shugabanta, sai Rauf Aregbasola a matsayin Sakatare.

Kaɗan daga cikin mutanen dake cikin wannan tafiya akwai Sule Lamido, Atiku Abubakar, Ameachi, Tambuwal, Goje da dai sauran su

Me zaku ce?

01/07/2025

Yadda aka gudanar da jana'izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata 😭

Mawaki Tuface Idibia, wanda aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa tsarin halittar namiji ya nuna cewa mace daya tayi masa...
01/07/2025

Mawaki Tuface Idibia, wanda aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa tsarin halittar namiji ya nuna cewa mace daya tayi masa kadan wajen saduwa.

Ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi kwanan nan da Nedu.

2Baba ya ce ko da maza na iya ƙaunar mace ɗaya da zuciyarsu gaba ɗaya, amma tsarin jikinsu bai basu damar kasancewa da mace ɗaya kawai ta fuskar jima’i ba.

Ya jaddada cewa wannan ba zabin mutum ba ne, sai dai wani bangare na asalin halittar namiji.

DA DUMI DUMI!!Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya jagoranci rushe wasu gine gine a kewayen filin sukuwa dake unguwar Nassar...
03/06/2023

DA DUMI DUMI!!

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif ya jagoranci rushe wasu gine gine a kewayen filin sukuwa dake unguwar Nassarawa a daren jiya Juma'a, wadanda aka yi lokacin Tsohuwar gwamnati.

Yayin aikin rusau din Gwamnan na tare da rakiyar kwamishinan yan Sandan Kano CP Muhammad Gumel da manyan jami'an gwamnati da kuma tarin jami'an tsaro.

Address

Kano
Abuja
700001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category