05/12/2025
Gwamnan jihar Neja Muhammad Umar Bago kenan a jiya Alhamis yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Mai Martaba Sarkin Zazzau Suleja Malam Muhammad Auwal Ibrahim bisa rashin matarsa Hajiya Rahama wadda ta rasu a ƙasar Masar (Egypt) a ƙarshen watan jiya.