
31/07/2025
HARIS DA HARISANCI
Kalmar HARIS a Larabci tana nufin MAI BAYAR DA TSARO, ko MAIGADI, wato mai bayar da kariya ga wani abu. Duk wanda ke tsaye yana kula ko bayar da kariya ga wani abu, sunansa Haris, idan suna da yawa ana ce musu HURRAS, a Hausance kuma jam’insu shi ne HARISAWA.
Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ne ya saka wa wasu gungun 'yan'uwa masu ƙoƙarin hidima wajen tsara muhallan tarurrukan Harka Islamiyya, kiyaye nizami yayin tarurrukan Harkan, da kuma bayar da tsaro wannan suna na HURRAS. Don haka ake kiransu da “Harisawan Harkar Musulunci.”
Haris ba kowa ba ne face ɗan’uwa daga cikin ‘yan’uwan da s**a samu baiwar fahimtar da’awar yunƙurin tabbatar da addinin Musulunci, kuma ya zaɓawa kansa ƙarin yin hidama ga addini da bayin Allah, ta hanyar sadaukar da kai don samar da tsaro da kiyaye nizami, tare da gadin Ingantacciyar Fikirar Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibrheem Zakzaky (H).
Saboda haka, aikin Harisanci shi ne aikin bada kariya, da tsayar da nizami, da kiyaye doka da oda a Harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bisa Fikirar Harkar, koyi da Amirulmuminin Ali Bin Abidalib (AS), wanda ya kasance babban HARIS ga Manzon Rahma (SA).
Shugaba kuma Jagoran Harisawa shi ne Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), saboda haka, wajibi ne kowane Haris ya sallama masa ɗari bisa ɗari a duk umurni da hani ko irshadinsa, wanda hakan zai gangaro zuwa ga bashi damar yin biyayya ga dukkan ƙa’idoji da dokokin aikin Harisanci. Da kuma umarni ko tsare-tsaren da za su riƙa zuwa masa daga Central ɗin aikin, wanda suna gangarowa ne daga irshadinsa (H).
Wajibi ne Haris ya zama akan gaba wajen baiwa Harka Islamiyya kariya ta janibin tsaron Fikira daga masu kutse, hujumi ko yunƙurin canzawa, da kuma tsaron Jagoran Harka da 'yan'uwa a yayin hujumin azzalumai a kowane lokaci, a kuma kowane waje. Haris mai sadaukar da lokacinsa, dukiyarsa da rayuwarsa ne don taimakon addinin Allah Ta'ala da hidimtawa Fikirar addinin ingantacce, wanda Jagora (H) ke da'awar tabbatarsa.
Haris shi ne mai amfani da hankali da dubi ga maslaha a wasu lokutan aikinsa da ya shafi hulda da jama’a, a wasu yanayoyi da halulluka na musamman, don kaucewa samar da matsala, ko haifar da mummunan sak**ako, ko natija marar ma’ana. Shi Haris mai kawo gyara ne a tsakanin mutane, ba za a taba samun Haris ya zama ɓangaren rigima ba, shi mai magance rigima ne. Ba zai zama mai azarɓaɓi ko gaban kansa wajen ɗaukar matakai masu tsauri ko sarƙaƙiya ba, ya kan zama a faɗake da dukkan motsi da shirin maƙiya ko ma'abota kuskure a kowane hali. Tsaurinsa na ga azzalumai ne, amma shi Haris rahama ne ga Muminai 'yan'uwansa.
Haris mai hidimar al'umma ne, da nuna musu jinƙai, da taimakonsu, da tausaya musu, da jikinsa, da dukiyarsa, da rayuwarsa gabaɗaya.
Haris mai ibada ga Allah Ta'ala ne, mai yin komai dominSa ne, mai kiyaye dokokinSa ne. Haris mutum ne ma'abocin kyawawan ɗabi'u, wanda maslahar addini ke danne son zuciyarsa a kowane lokaci da hali.
Yi ƙoƙari ka zama, ko ki zama daga cikin Harisawan Harkar Musulunci a aikace, ba kawai a amsa sunan da rakiyar tafiyar ba. Allah Ta'ala Ya sanya mu zama daga cikin Harisawan addininSa. Ilahi Ameen.
NI HARIS NE.
— Hurrasul Harakatil Islamiyya
6 Safar, 1447 (31/7/2025)