Wata Shari a,Sai Alahira

Wata Shari a,Sai Alahira Wata Shari a,Sai Alahira jarida ce dazata rika kawo muku labarai na gida Najeriya dama na wasu sassan Duniya

NEMAN TEMAKOjama a atemaka domin yiwa wan nan yaro aikin idoKAI JAMA A IDAN BAKA MUTUBA BAKA GAMA GANIN KOMIBAWan nan ya...
26/06/2026

NEMAN TEMAKO
jama a atemaka domin yiwa wan nan yaro aikin ido

KAI JAMA A IDAN BAKA MUTUBA BAKA GAMA GANIN KOMIBA

Wan nan yaro mai Suna Sani yana bukatan temako ga bayin Allah ga Wanda Allah yabawa iko domin yimishi aikin ido

yana fama da cutar daji wanda akecewa dashi(Cancer) a idanshi na dama.Idon yariga da ya rufe saboda wan nan cuta da idan nashi dayan idan na haguma basosai yake gani dashiba

yanzu haka Suna Hospital na ido Kankara dake katsina.Likitoci sunbada tabbacin cewa idan ba ayimishi aikin wan nan idan nashiba dayan idan ma zai iya lalacewa yadena gani gaba daya.

A halinda ake ciki Mahaifiyar yaran batada karfin daukar nauyin aikin daza ayimishi sakamakon mahaifin yaran yarasu,yan uwan mijin nata sunbarta da dawainiya basuko temakonta saboda margayi mijin nata bashida komai talakane har Allah yayi mishi rasuwa.

Jama a,basai angayaba wasu yan uwa basu temakon yan uwa tun Suna Raye b***e sun rasu.Haka yasa mukaga dacewa domin nemamusu temako ga bayin Allah mai taro siri atemaka domin yiwa wan nan yaro aikin wan nan cuta.

Ga Account Number daza a tura temako duk Wanda yayi niya yayi amfani dashi wajen saka temakonshi.

9030300320 OPAY
Suleiman Sango

Allah yabashi lafiya,Allah yabada ikon temakawa Amin

CIGIYA: Ana Cigiyar Wannan Matashiya Mai Suna  Ummulkhairi Awaisu Zubairu Dake Unguwar Ƙofar Gabas A Ƙaramar Hukumar Gar...
06/06/2026

CIGIYA: Ana Cigiyar Wannan Matashiya Mai Suna Ummulkhairi Awaisu Zubairu Dake Unguwar Ƙofar Gabas A Ƙaramar Hukumar Garin Malam, Jihar Kano Da Ta Bar Gida Da Yammacin Jiya Laraba Har Yanzu Babu Labarin Ta.

Duk Wanda Allah Ya Sa Ya Ganta Yana Iya Tuntuɓar Wannan Lambar Domin Ƙarin Bayani

08104388796

Allah Ya Sa A Dace!

Da ɗumi-ɗumi: Shugaba Bola tinubu yafi Sardauna da Tafawa balewa darajar a idona don haka ya zama dole 'yan Arewa su sak...
06/06/2026

Da ɗumi-ɗumi: Shugaba Bola tinubu yafi Sardauna da Tafawa balewa darajar a idona don haka ya zama dole 'yan Arewa su sake zaɓen sa a zaɓen 2027 –Sani Zangina

Shugaban Tawagar goyon bayan sake zaɓen shugaba Bola tinubu a Arewa ya daga darajar Bola Ahmed Tinubu kan dattijan Arewa da s**a shuɗe a ƙoƙarin sa na tallata shugaba Tinubu don ganin 'yan Arewa sun sake zaɓen sa a zaben 2027.

Hon Sani Ahmad Zangina ya bayyana cewa kawo yanzu yafi ganin darajar shugaba Bola tinubu fiye da duk wani dattijon Arewa na wanda ke raye da wanda ya rasu ya kara da cewa darajar da yake kallon shugaba Tinubu Tinubu xa ita yafi Sardauna yafi Amimu Kano yafi Tafawa balewa da IBB yana bayyana cewa Wajibi ne ga ɗan arewa ya sake zaɓen shugaba Tinubu a zaɓen na 2027

GIDAUNIYA ATEMAKAWA MARAYUGAMASU SAN TALLAFAWA MARAYU KO ZAKKA Ayi amfani da wan nan dama don bada tallafiZa ayi Launchi...
08/03/2026

GIDAUNIYA ATEMAKAWA MARAYU
GAMASU SAN TALLAFAWA MARAYU KO ZAKKA
Ayi amfani da wan nan dama don bada tallafi

Za ayi Launching gobe lahadi 19 ga wan nan watan Ramadan zuwa 20 21 insha Allah

Gamasu bukatar temakawa da abinda Allah yahore

KAYAN SAWA KO
ABINCHI KO
SABULAI KO
KUDI daza araba musu

Za a iya tura tallafi ga MARAYU ta wan nan Asusun banki account

account number--0727292929
Suwaiba Muhammad Usman

GT Bank

Allah yasaka da alheri

Ban taba yin nadamar Taimakawa wani a masana'antar kannywood ba, koda ace nayi silar ya zama wani daga baya kuma yaci am...
05/03/2026

Ban taba yin nadamar Taimakawa wani a masana'antar kannywood ba, koda ace nayi silar ya zama wani daga baya kuma yaci amanata cewar Ali Nuhu.

Fitaccen jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana cewa bai taba yin nadamar taimakawa kowa a harkar fim ba, ko da kuwa daga baya wanda ya taimaka ya juya masa baya.

Jarumin ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wani dan jarida, inda aka tambaye shi ko yana jin nadamar yadda ya dauki matasa da dama ya horas tare da daga su a masana’antar, amma wasu daga cikinsu s**a ci amanarsa. Amsarsa ta kasance mai cike da hikima da karfin zuciya.

A cewarsa: “Ban taba yin nadamar taimakawa wani a masana’antar Kannywood ba, koda ace nayi silar ya zama wani daga baya kuma yaci amanata.” Ya kara da cewa duk taimakon da mutum ke yi, Allah ne tun farko ya rubuta zai yi shi, don haka bai kamata a dora shi a kan nadama ba.

Ali Nuhu ya jaddada cewa taimako ibada ne, kuma duk wanda ka taimaka masa, hakan wani bangare ne na kaddarar da Allah Ya tsara tun kafin faruwar lamarin. “Idan ka taimaka wa mutum ya zama wani, to ka zama silar alheri ne kawai. Idan kuma daga baya ya sauya, wannan shima yana cikin jarabawar rayuwa,” in ji shi.

Maganar tasa ta sake nuna matsayin jarumin a matsayin uba a masana’antar Kannywood, wanda ya shahara wajen bai wa matasa dama da goyon baya domin cimma burinsu. Duk da kalubalen da ake samu a harkar, Ali Nuhu ya nuna cewa zuciyarsa a bude take wajen ci gaba da tallafawa masu tasowa, ba tare da kallon abin da zai biyo baya ba.

Wannan furuci nasa ya janyo martani daga masoya da abokan aikinsa, inda da dama s**a yaba da halinsa na yafiya da kuma daukar al’amura da kaddara.

Shari a sai alahira jarida

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi gargaɗi mai kaushi kan ƙasashen Am0ruƙa da 1$ra£| yana ma...
04/03/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi gargaɗi mai kaushi kan ƙasashen Am0ruƙa da 1$ra£| yana mai cewa abin da suke aikata wa 1rán za|uπci ne, kuma suna gab da ƙetare jan layi.

Shugaban ya ce yana kan tattaunawa da shugaban ƙasar China da kuma shugaban ƙasar Rasha kan yiyuwar shigarsu ¥aƙin dumu-dumu muddin Am0ruƙa da 1$ra£| s**a ƙetare jan layi.

Ya kuma yi wa musulman duniya ta'aziyyar jag0ra Ayat0llah Kham£n£i inda ya bayyana shi a matsayin gwarzon duniya wanda ba kasafai ake samun mutane masu jarumtarsa ba.

Idan ka ji daɗin labarin ka dangwala mana like sannan ka yi mana share.

Me za ku ce?

Ku yi following ɗin jaridar Wata shari a sai alahira
Hausa domin samun sahihan labarai masu daɗi da gamsarwa

🔥 IRAN TA SHIGA TARIHI 🇮🇷🇨🇾Jirgin yaƙin mara matuƙi na Iran mai suna Shahed ya yi tafiyar kusan kilomita 2,000 ta cikin ...
04/03/2026

🔥 IRAN TA SHIGA TARIHI 🇮🇷🇨🇾

Jirgin yaƙin mara matuƙi na Iran mai suna Shahed ya yi tafiyar kusan kilomita 2,000 ta cikin Tekun Bahar Rum (Mediterranean Sea) sannan ya kai hari kan sansanin sojin sama na Birtaniya wato RAF Akrotiri da ke Cyprus, kuma babu ko ɗaya daga cikin tsarin kariyar sararin samaniyar NATO da ya gano shi.

Wannan ita ce Iran ɗin da aka kakabawa takunkumi, aka kai mata hare-hare, aka ware ta tsawon shekaru da dama — amma jiragenta marasa matuƙi da makamai masu linzami sun iya kutsawa cikin mafi tsaron sararin samaniya a duniya.

Bayan Amurka da Isra’ila sun kai hari kan Tehran tare da kashe Jagoran Ƙoli Ali Khamenei, Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan ƙasashe 15, sansanonin sojin Amurka 27, sannan yanzu ma da wani sansanin Birtaniya a Cyprus — duk a cikin sa’o’i 24.

A fayyace yake: babu wata rundunar soja a duniya da ta taɓa yin irin wannan.

Yammacin duniya ya gina tsarin kariya na biliyoyin daloli. Iran kuwa ta gina ƙudurin wucewa ta cikinsu.

Duniya ba za ta sake zama iri ɗaya ba bayan yau.

Bazawara Mai shekara 30 yar asalin garin Bichi mazauna Unguwar Jadaka, Mai aikin gwamnati (state level), tana da yarinya...
03/03/2026

Bazawara Mai shekara 30 yar asalin garin Bichi mazauna Unguwar Jadaka, Mai aikin gwamnati (state level), tana da yarinya daya, tana da karatun Addini Mai zurfi. tana neman mijin aure responsible mutum koda Wanda ya shirya aure Bayan salla ne.
Ga hotonta nan munsa kamar yadda ta amince.

Gawanda keda bukata da gaske yamana magana ta Comment Section San nan a danna mana following da liking

03/03/2026
Da ɗumi-ɗumi: Isra’ila Ta Mayar da Jirgin Gwamnati Zuwa Jamus Saboda Tsaro bayan Iran tana kan lugudan wuta kan ƙasar. G...
02/03/2026

Da ɗumi-ɗumi: Isra’ila Ta Mayar da Jirgin Gwamnati Zuwa Jamus Saboda Tsaro bayan Iran tana kan lugudan wuta kan ƙasar.

Gwamnatin Isra’ila ta mayar da jirginta na musamman da ake amfani da shi wajen jigilar manyan jami’an gwamnati zuwa ƙasar Jamus domin dalilan tsaro.

Mai magana da yawun shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, yana mai cewa an ɗauki matakin ne a ƙarshen makon da ya gabata.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin gwamnatin Isra’ila — wanda ake amfani da shi wajen jigilar shugaban ƙasa da firaminista — an kwashe shi zuwa Jamus ne domin kauce wa duk wata barazana ta tsaro a daidai lokacin da rikici ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

Matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tashin hankali tsakanin Isra’ila da Iran, lamarin da ya sanya ƙasashe da dama ke ɗaukar ƙarin matakan tsaro domin kare muhimman kadarorinsu.

Har yanzu dai ba a bayyana tsawon lokacin da jirgin zai ci gaba da kasancewa a Jamus ba.

Address

Zone3
Abuja
304060

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wata Shari a,Sai Alahira posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Wata Shari a,Sai Alahira:

Shortcuts

Share