
02/07/2025
YADDA ZAKA GIRMAMA KANKA DA KANKA.
1. Ka Dena Neman Wanda baya Neman ka.
2. Ka Dena Maula a Wajen Mutane.
3. Ka Dena Surutu Fiye Da Yadda Ya Kamata.
4. Idan Mutum ya Wulakanta Ka, Koda a Rashin Sani Ne ka Sanar Dashi Kai Tsaye.
5. Ka Dena fada da mutane, Karkayi cuta .
6. Kayi adalci akan Kowa da Kowa, Kai Koda baka San Mutum bah.
8. Ka guji cuta, da cutarwa.
9. Ka zama Mai yada Alkhairi a rayuwar ka Baki Daya.
10. Mu Dinga Yiwa Yan Uwan mu Kyaukyawan Zato.
11. Kada ka dinga yiwa Yan uwan ka mummunan zato.
12. Ka Dena Zagin shuwagabanninka, addu'a ya dace muyi musu.
13. Kayi Alaqa da mutane da kyaukyawan Dabi'a.
14. Ka zama Mai yawan sakin Fuska, kada Ka dinga hada Fuska . Dan Annabi yace ka hadu da Dan uwan ka kana masa murmushi ma sadaka ce.
15. Karkayi wasa da Al qur'ani, Al qur'ani babban kundi ne Al qur'ani nitsuwane Al qur'ani Ibadah ce Al qur'ani maganar Allah ce Al qur'ani sai Mai Rabone zai rika samun damar karantashi.
19. Kanemi Aljannah Kuma Aljannatul firdausi zaka Fi nema .
20. Kaji Tsoron Allah a duk Inda kake .
Ina muku fatan Alkhairi, Allah ubangiji ya Saka muku da gidan Aljannatul firdausi fatan Alkhairi a gareku Yan uwana Masu Albarka.
Kayi Sharing zuwa ga Yan uwa Dan Suma su Anfana.
Allah sa muyi kyaukyawan karshe