11/08/2026
Babban Kwamandan Rundunar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Takai, Ustaz Ahmad Musa, ya yi Allah-wadai da zargin cewa an karɓi kuɗi daga hannun waɗanda aka ɗaura wa aure a ƙarƙashin Shirin Auren Gata na Ƙaramar Hukumar Takai.
Arewa Albishir ta rawaito cewa, Mataimaki na Musamman kan Kafofin Yaɗa Labarai na Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Takai da Sumaila, Rabiu Yusuf, Sagir Sabo Kachako, ne ya wallafa bayanin a shafinsa na Facebook. Ustaz Ahmad Musa ya ce zargin ya ba shi mamaki, yana mai cewa duk wanda ke da hujjar cewa an karɓi kuɗi ya gabatar da ƙorafinsa ga Hukumar, tare da bayyana wanda ya ba da kuɗin ko wanda ya karɓa.
Kwamandan ya bayyana cewa Hisbah, tare da haɗin gwiwar Ƙaramar Hukumar Takai, ce ta ɗauki nauyin zirga-zirgar ɗauko kayan amare da ango daga Kano zuwa Takai, ba tare da neman ko sisi daga hannun ma’auratan ba. Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala ɗaurin auren a Babban Masallacin Jumu’a na Cikin Garin Takai, ranar Juma’a 7 ga Agusta, 2026.
A ƙarshe, Ustaz Ahmad Musa ya yi kira ga al’umma da su guji yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, musamman waɗanda ke da alaƙa da siyasa, yana mai jaddada muhimmancin bincike da tabbatar da gaskiyar labari kafin yaɗa shi.