07/08/2026
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya karɓi rahoton kwamitin da aka kafa domin duba hanyoyin yin garambawul da farfaɗo da ilimin matakin farko da na fasaha a jihar.
Gwamnan ya bayyana rahoton a matsayin muhimmin tsari da zai taimaka wajen sauya fasalin harkokin ilimi tare da inganta koyo da koyarwa da kuma samar da matasa masu ƙwarewar da za su iya fuskantar buƙatun kasuwar aiki a nan gaba.
Yayin karɓar rahoton, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa za ta fara nazarin shawarwarin da ke cikin rahoton nan take, tare da ɗaukar matakan aiwatar da su.
Ya ce, “Game da wannan rahoto, ina tabbatar muku cewa ba za mu yi watsi da shi ba. Za mu nazarce shi nan take sannan mu fara aiwatar da shawarwarin da ke cikinsa.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa tuni gwamnatinsa ta fara yin wasu manyan sauye-sauye a tsarin harkokin ilimi, ciki har da haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi zuwa ma’aikata guda.
A cewarsa, wannan mataki zai ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin sassa daban-daban na ilimi, da kuma sauƙaƙa aiwatar da manufofi da samar da ingantaccen aiki a fannin.
Gwamna Inuwa ya ce tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019, gwamnatinsa ta fuskanci matsaloli da dama a fannin ilimi, amma ta samu nasarori ta fuskar gine-ginen makarantu, bunƙasa ƙwarewar malamai, ƙara yawan ɗalibai, faɗaɗa damar samun ilimi da kuma sauye-sauyen tsarin gudanarwa.
Ya sake jaddada alkawarin da ya ɗauka na cewa gwamnatinsa za ta bar Jihar Gombe cikin yanayi mafi kyau fiye da yadda ta same ta, musamman a ɓangaren ilimi.
“Mun san irin yanayin da muka tarar da wannan fanni lokacin da muka zo mulki a 2019. Muna godiya ga Allah cewa mun samu nasarori masu yawa. Ina sake jaddada alkawarin da na yi cewa za mu bar Gombe fiye da yadda muka same ta a ɓangaren ilimi,” in ji shi.
Da yake magana a madadin kwamitin, fitaccen masani kan harkokin ilimi kuma tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Tom Mataimaki Maiyashi, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa kafa kwamitin da kuma nuna kishin kawo sauyi a fannin ilimi.
Maiyashi ya ce rahoton ya kunshi cikakken bayani kan halin da ilimin matakin farko da na fasaha ke ciki a Gombe, tare da shawarwari masu amfani waɗanda za a iya aiwatar da su.
Ya bayyana cewa idan aka aiwatar da shawarwarin rahoton yadda ya kamata, hakan zai taimaka matuka wajen sauya tsarin ilimi na jihar tare da sanya Gombe cikin jihohin da ke kan gaba wajen samar da ingantaccen ilimi.
A nata bayanin, Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe kuma shugabar kwamitin, Assoc. Prof. Aishatu Umar Maigari, ta ce an kafa kwamitin ne a watan Nuwamba 2025 domin yin cikakken nazari kan halin da ilimin matakin farko da na fasaha ke ciki a jihar.
Ta ce kwamitin ya duba batutuwan da s**a shafi ƙalubalen malamai, ƙarancin gine-ginen makarantu, tsarin gudanarwa, jin daɗin ɗalibai, yanayin koyon karatu, tsaro da kuma rawar al’umma wajen tallafawa harkokin makarantu.
A cewarta, sakamakon binciken ya zama tushen samar da shawarwari da aka tsara cikin manyan rukunan gyara guda takwas, waɗanda ke buƙatar kulawar gwamnati cikin gaggawa domin samun ci gaba mai ɗorewa a fannin ilimi.
Kwamishiniyar ta yaba da yadda Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna ƙwarin gwiwa da kishin ilimi ta hanyar kafa kwamitin da ya ƙunshi ƙwararru da masana masu dogon tarihi a fannin.
Kwamitin ya ƙunshi manyan masana da masu tsara manufofin ilimi, ciki har da Assoc. Prof. Aishatu Umar Maigari, Dr. Nura A. Yakubu, OON, tsohon Babban Sakataren National Board for Technical Education (NBTE), Dr. Hamid Bobboyi, tsohon Babban Sakataren Universal Basic Education Commission (UBEC), Tom Mataimaki Maiyashi, Dr. Sadiq Gombe, Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Gombe, da kuma Babban Sakataren dindindin na Special Services and Political, Government House, Gombe.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke ƙara mayar da hankali wajen sake fasalin tsarin ilimi domin inganta ingancin makarantu, malamai da kuma makomar ɗaliban Jihar Gombe.