
31/08/2025
Gwamna Uba Sani ba Abokina bane Amma Almajiri na ne -El Rufa'i.
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ba abokinsa ba ne, sai dai almajirinsa (mentee). El-Rufa’i ya ce:
“Uba Sani ba abokina ba ne, shi dai ‘boy’ ɗina ne, saboda na ba shi tarbiyya a siyasa, don haka kawai nake kiransa aboki.”
Da mai gabatar da shirin Seun Okinbaloye ya tambaye shi cewa, “Shin har yanzu kuna magana da shi?”
Sai El-Rufa’i ya amsa da cewa a'a
ELTAF News TV