01/04/2023
Ana Neman Taimakon Gaggawa: Don Allah Jama'a Ku Taimaka..........................................................
Mustafa Abdulkarim dalibi ne mai hazaka da kwazo ga kokari da biyayya ga malamai na dukkan bangarorin boko da islamiyya a lokacin da yake zuwa makaranta cikin koshin lafiya kafin ya hadu da jarabawa ta rayuwa.
Mustafa yana zaune tare da iyayen shi a bayan mishau kusa da masallacin Abu Jalli Gambo dake cikin garin Malumfashi. Ga shi ya gamu da babbar jarrabawa sanadiyyar rauni da yayi a hannun shi na hagu sakamakon faduwa da yayi wanda daga bisani ciwon ya rikida ya koma kamar yadda kuke ganin shi acikin hoton wanda ake tunanin ciwon daji ne.
Iyayen Mustafa sunyi bakin kokarin su wajen yi mashi magunguna kala-kala na gida da na asibiti amma ciwon yaki ci yaki cinyewa yanzu haka maganar da ake Mustafa yana akan magungunan asibiti ne da likita ya dora shi akai, gashi kuma yanzu halin da ake ciki magani ya kare ga karfin iyayen Mustafa ya kare kasancewar basu da karfi. Mustafa baya da wani gata sai Allah sai ku idan kun taimaka mashi. Yanzu haka yana bukatar ledojin jini kamar yadda asibitin s**a fada gashi babu abin siya babu dalilin su.
Saboda haka ne ake neman taimakon ku yanuwa don Allah a taimaka ma wannan yaro da iyayen shi domin shawo kan wannan matsala da ta same shi.
Taimako bashi da yawa bashi da kadan, don Allah ku taimaki wannan yaro Mustafa don alfarmar Annabi da Alqur'ani da wannan wata na Ramadana da muke ciki.
Ga Account da akayi tanaji domin tara kudin taimakon
Account No.: 0690429567
Account Name: MuntΓ ri Abdullahi
Bank: Access Bank
Allah ya bada ikon taimakawa. Amin
Mai neman karin bayani ya kira wadannan lambobin dake kasa.
07069497814
09077467506