27/08/2026
ABUJA: Kotu Ta Tura Faruk Abuja Gidan Yarin Kuje Kan Zargin Cin Zarafin Ministan Tsaro
An gurfanar da fitaccen ɗan TikTok kan tuhume-tuhume guda huɗu, yayin da aka ɗage sauraron buƙatar belinsa zuwa 9 ga Satumba
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare fitaccen ɗan TikTok, Faruk Musa Muhammad, wanda aka fi sani da Faruk Abuja, a gidan yarin Kuje bisa zargin cin zarafin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ta kafar intanet. An gurfanar da Faruk mai shekaru 35 a gaban Mai Shari’a Obiorah Egwuatu kan tuhume-tuhume guda huɗu.
Ana zargin Faruk da wallafa wasu kalamai da s**a yi ikirarin cewa sojojin Najeriya da ke yaƙi da ta’addanci na rasa rayukansu sakamakon gazawar Ministan Tsaro da shugabannin hukumomin tsaro wajen ɗaukar matakan da s**a dace. Haka kuma, tuhume-tuhumen sun ƙunshi wasu zarge-zarge da s**a shafi Mai Bai wa Ministan Shawara kan Harkokin Shari’a, Aliyu Anas.
Faruk ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa. Lauyansa, Abdulkadir Ahmad, ya kuma sanar da kotun cewa yana da niyyar neman a bayar da belinsa. Sai dai Mai Shari’a Egwuatu ya ɗage sauraron buƙatar belin zuwa 9 ga Satumba, 2026, tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare Faruk a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin.