18/09/2026
JAGORAN ANSARULLAH NA YEMEN, SAYYID ABDUL-MALIK AL-HOUTHI, YA GABATAR DA JAWABI KAN ABUBUWAN DA KE FARUWA A KASAR TA YEMEN.
– Ya ce hare-haren da Saudiyya ke kai wa al’ummar Yemen ne tushen halin da ake ciki a yanzu.
Ya ce haryanzun al’ummar Yemen suna matakin kare kansu daga hare-haren Saudiyya ne.
Ya kuma bayyana cewa Yemenawa na kare ƙasarsu da mutuncinsu daga hare-haren Saudiyya.
Ya ce rundunar Yemen tana kai hari ne kawai kan barukokin soji.
Ya bayyana cewa Sojojin Yemen na kare ikon mallakar ƙasar da cikakken yankinta daga hare-haren Saudiyya.
Jagoran Ansarullah ya zargi Saudiyya da kai hari kan fararen hula, ababen more rayuwar jama’a, masallatai da filayen jiragen sama a Yemen.
Ya bayyana cewa lallai Saudiyya ta aikata manyan laifuka kan al’ummar Yemen.
Ya ce an tattara tare da rubuta bayanan laifukan yaƙi da Saudiyya ta aikata kan Yemenawa.
Ya bayyana cewa Saudiyya na ƙoƙarin durƙusar da Yemen a fannoni daban-daban a lokacin da ake samun raguwar tashin hankali.
–ABS Radio Hausa.