11/06/2026
Cikakken Bayani Kan Kudirin Dokar Kafa ’Yan Sandan Jihohi da na Tarayya a Najeriya
Majalisar Dokokin Najeriya na ci gaba da nazarin wasu gyare-gyaren kundin tsarin mulki da za su ba da damar kafa tsarin ’yan sanda biyu a ƙasar, wato ’Yan Sandan Tarayya (Federal Police) da kuma ’Yan Sandan Jihohi (State Police).
Kafa ’Yan Sandan Tarayya da na Jihohi
Sabuwar dokar da ake son yi za ta tanadi kafa rundunar ’yan sandan tarayya da kuma rundunar ’yan sanda a kowace jiha. Sai dai rundunar ’yan sandan jiha ba za ta fara aiki ba har sai majalisar dokokin jihar ta amince da ita tare da cika ƙa’idojin ƙasa da Majalisar Tarayya ta gindaya.
A jihohin da ba su kafa rundunar ’yan sandansu ba, rundunar ’yan sandan tarayya za ta ci gaba da gudanar da dukkan ayyukan tsaro.
Ayyuka da Iyakokin Ikon Kowace Runduna
Rundunar ’yan sandan tarayya za ta kasance mai kula da tsaro da tabbatar da doka da oda a faɗin ƙasa.
Sai dai an sanya kariya domin hana gwamnatin tarayya tsoma baki cikin harkokin tsaron jihohi sai a lokuta na musamman, kamar:
Idan doka da oda sun rushe gaba ɗaya a wata jiha.
Idan gwamnan jiha ya nemi taimako.
Idan rundunar ’yan sandan jihar ta kasa gudanar da aikinta saboda matsalolin kuɗi ko gudanarwa.
Duk wani irin shiga tsakani daga gwamnatin tarayya sai da amincewar Majalisar Kula da ’Yan Sanda ta Ƙasa.
Shugabanci da Naɗin Manyan Jami’ai
Rundunar ’yan sandan tarayya za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (IGP) wanda shugaban ƙasa zai naɗa tare da amincewar Majalisar Tarayya.
A ɓangaren jihohi kuwa, kowace rundunar jiha za ta kasance ƙarƙashin Kwamishinan ’Yan Sanda (CP) wanda gwamna zai naɗa tare da amincewar Majalisar Dokokin Jiha.
Yadda Za a Cire Shugabannin Rundunonin
Sabuwar dokar ta tanadi cewa ba za a iya cire Sufeto Janar ko Kwamishinan ’Yan Sanda daga mukamansu ba sai bisa wasu dalilai da s**a haɗa da rashin ɗa’a, karya doka, zamba, ko rashin lafiyar da ta hana gudanar da aiki.
Haka kuma, cire su zai buƙaci amincewar kashi biyu bisa uku na mambobin majalisun dokoki.
Tallafin Kuɗi Ga Jihohi
Gwamnatin Tarayya za ta iya bai wa jihohi tallafin kuɗi domin taimaka musu wajen tafiyar da rundunonin ’yan sandan jihohi, bayan amincewar
Majalisar Tarayya.
Sabbin Hukumomin Kula da Rundunonin
An kuma tanadi kafa sabbin hukumomi da za su kula da ayyukan rundunonin ’yan sanda, ciki har da:
Majalisar Kula da ’Yan Sanda ta Ƙasa.
Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sandan Jiha a kowace jiha.
Waɗannan hukumomi za su kula da naɗi, horo, bincike da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin aiki.
Ikon Majalisun Tarayya da Jihohi
Majalisar Tarayya za ta tsara ƙa’idojin ƙasa da dokokin da za su jagoranci ayyukan rundunonin ’yan sanda.
A lokaci guda kuma, majalisun dokokin jihohi za su iya kafa dokokin tafiyar da rundunonin jihohinsu muddin ba su saɓa wa
kundin tsarin mulki da dokokin ƙasa ba.
Muhimman Sauye-Sauye
Kudirin ya kuma tanadi gyare-gyare a wasu sassan kundin tsarin mulki domin maye gurbin tsohon tsarin rundunar ’yan sanda guda ɗaya da sabon tsarin rundunonin tarayya da na jihohi.
Masu goyon bayan kudirin na ganin cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro cikin sauri saboda kusancin jami’an tsaro da al’ummomin yankunansu.
Sai dai wasu na nuna damuwa kan yiwuwar amfani da rundunonin wajen manufofin siyasa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba. :::
Wannan shi ne cikakken bayani kan kudirin dokar da ake son yi domin kafa ’Yan Sandan Jihohi da na Tarayya a Najeriya.
Hoto: Katsina daily news