02/12/2024
In ban da rashin sani, dokar harajin Tinubu ribar ƙafa ce ga Ƴan Arewa - Jibrin Kofa
“A tarihin Najeriya wannan ne karon farko da za a cire wa talaka harajin VAT daga kan kayan abinci.”
Premium Times Hausa
In ban da rashin sani, dokar harajin Tinubu ribar ƙafa ce ga Ƴan Arewa – Jibrin Kofa
Premium Times HausabyPremium Times Hausa December 1, 2024
In ban da rashin sani, dokar harajin Tinubu ribar ƙafa ce ga Ƴan Arewa – Jibrin Kofa
A yayin da ake cigaba da dambarwa kan batun sake fasalin haraji a Najeriya da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta gabatar wa da majalisun ƙasar domin neman sahalewarsu.
Ana cigaba da samun ra’ayoyi mabambanta da ke nuna goyon baya ko s**ar waɗannan ƙudurori.
Abdulmumini Jibrin Kofa, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Kano ya ce ko kaɗan babu wani abin cutarwa tattare da ƙudurorin dokar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da musu da shi a majalisa.
Kofa ya ce, “na shafe shekaru huɗu a matsayin shugaban kwamitin kuɗi, don haka ba abu ne nake yi da ka ba. In ga kaso kusan 90 da suke cikin wannan sabuwar dokar, abubuwa ne da muka daɗe tun ina ciyaman na kwamitin kuɗi, muke ta ƙoƙarin gwamnatin tarayya ta yi. A canza dokar harajin Najeriya a sanya waɗannan abubuwa kuma waɗannan abubuwa da ake magana, wallahi tallahi ba abubuwa ne da za su cutar da talaka ba.” in ji Kofa.
Haka kuma ya ƙaryata batun da ake na an ƙara wa talaka haraji a wannan doka, inda ya ce wannan zargi ba gaskiya ba ne.
Kofa ya ce, “sake fasalin haraji abu ne da zai shafi dukkan jihohin Najeriya ba wai iya Arewa ba.”
Sannan ya ce akwai alfanu mai yawa da talaka zai samu idan aka tabbatar da wannan ƙuduri. Ya buga misali da cewa, “A tarihin Najeriya wannan ne karon farko da za a cire wa talaka harajin VAT daga kan kayan abinci.”
Ya ce hatta harkar ilimi da lafiya duk an cire musu harajin VAT.
Har’ila yau ya ce, talaka zai samu tagomashi ta fuskar mafi ƙarancin albashi da aka yi a kwanakin baya, domin duk wanda albashinsa mafi ƙarancin ne, to ba zai