17/08/2026
DA DUMI-DUMI: Tsohon Dan Takarar Gwamnan Jihar Gombe Sanata Amb. Haruna Garba, Ya Goyi Bayan Pantami, Ya Kuma Mika Cikakken Tsarin Siyasarsa Ga Professor Isa Ali Pantami
Mai girma Ambasada Sanata Haruna Garba ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Professor Isa Ali Pantami, CON, (Majidadin Daular Usmaniyya), tare da mika masa tsarin siyasarsa. Haka kuma, ya umarci magoya bayansa da su hada kai da Farfesa Pantami domin tunkarar zaben 2027 da abin da zai biyo baya.
Sanata Haruna Garba ya wakilci Gombe ta Arewa a Majalisar Dattawa daga shekarar 2003 zuwa 2007. Daga shekarar 2012 zuwa 2015 kuma ya kasance Jakadan Najeriya a Kuwait. Haka kuma, ya yi takarar gwamnan Jihar Gombe a zaben shekarar 2019.
Sanata Haruna Garba shi ne Akanta-Janar na farko na jihar Gombe, sannan ya taba zama Kwamishinan Kudi na jihar.
An san Sanata Haruna Garba a matsayin daya daga cikin manyan masu taimakon al’umma da jihar Gombe ta samar, inda ya taimaka wa mutane da dama tare da sauya rayuwarsu.
Babban dalilin da ya sa ya goyi bayan Farfesa Isa Ali Pantami shi ne irin kyakkyawan aikin da Pantami ya yi a dukkanin mukaman da ya rike a baya. Hakan ya hada da lokacin da yake Darakta-Janar na Hukumar NITDA da kuma lokacin da yake Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani.
A cewar sanarwar, Farfesa Pantami ya taimaka wajen sauya wasu cibiyoyi daga halin durkushewa zuwa zama cikin manyan cibiyoyi a kasar. Haka kuma, an bayyana alakar sa da kasashen duniya a matsayin wata babbar dama ga Najeriya baki daya, ba Gombe kadai ba.
An kuma bayyana cewa Farfesa Pantami ya taba shugabantar Global ICT and Digital Ministers, inda ya jagoranci ministoci 193 daga kasashe daban-daban tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023.
Sanarwar ta kara da cewa Pantami ya tabbatar da kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana, a lokacin da yake cikin gwamnati da kuma bayan barin mukaman gwamnati.
A cewar Sanata Haruna Garba, zaɓen Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami bisa la’akari da gaskiyarsa, amincinsa, kwarewarsa, kyakkyawan tarihin aikinsa, alakar cikin gida da ta kasa da kasa, da kuma iliminsa, zai kasance babbar dama ga Jihar Gombe da Najeriya baki daya.
A karshe, Sanata Haruna Garba ya mika cikakken tsarin siyasarsa ga Farfesa Pantami, tare da neman su yi aiki tare. Ya kuma yi alkawarin ci gaba da hada kai da sauran masu ruwa da tsaki domin mara wa takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami baya, da nufin gina Jihar Gombe mai ci gaba da amfani ga kowa.
Farfesa Suleiman Mohammed
(A madadin Pantamiyya Movement ta Najeriya)