14/03/2026
🇷🇺🇮🇷 Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, na shirin ganawa da sabon Jagoran Ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei, karo na farko.
Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya bayyana a wata hira da kamfanonin labarai na Rasha cewa ana sa ran ganawar farko kai tsaye tsakanin Putin da sabon Jagoran Ƙolin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, za ta iya gudana daga baya a wannan shekarar.
A cewar Jalali, ana sa ran ganawar za ta kasance ne a yayin taron ƙasashen da ke kewaye da Tekun Caspian Sea, wanda Iran za ta karɓi bakuncinsa a ranar 12 ga Agusta, 2026, a birnin Tehran.
Taron zai haɗa shugabannin ƙasashen da ke kewaye da Tekun Caspian, kuma ana ganin zai zama dama ta farko da manyan shugabannin Moscow da Tehran za su yi ganawar kai tsaye tun bayan da Mojtaba Khamenei ya hau kan jagorancin ƙasar Iran.
Har ila yau, Jalali ya bayyana cewa Mojtaba Khamenei mai shekaru 56 yana cikin ƙoshin lafiya, kuma a shirye yake ya jagoranci Iran a wani lokaci da ya ce ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale