labarai da rahotanni

labarai da rahotanni labarai da rahotanni

YANZU-YANZU:Atiku Abubakar Ya Yi Alkawarin Buɗe Iyakokin Najeriya Don Shigo Da Kayan Abinci Da Fadada Kasuwanci Tsakanin...
27/08/2026

YANZU-YANZU:Atiku Abubakar Ya Yi Alkawarin Buɗe Iyakokin Najeriya Don Shigo Da Kayan Abinci Da Fadada Kasuwanci Tsakanin Makota

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa idan ya samu damar jagorantar Najeriya, zai sake buɗe iyakokin ƙasar, domin farfaɗo da harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da ƙasashen makwabta.

Atiku ya ce zai ƙarfafa cinikayyar ƙetare, inganta kasuwancin yankin da kuma rage nauyin matsin tattalin arziki da ke kan ’yan Najeriya da ’yan kasuwa.

A cewarsa, manufarsa ita ce a samar da yanayin da zai bai wa ’yan kasuwa damar gudanar da halastaccen ciniki cikin sauƙi, tare da faɗaɗa damar samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙarfafa dangantakar kasuwanci tsakanin Najeriya da ƙasashe makwabta.

Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ƙarin damammaki ga al’ummar Najeriya.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a lokacin da yake bautar ƙasa (NYSC) a shekarar 1989/1990.An gyara hoton (an ingan...
26/08/2026

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a lokacin da yake bautar ƙasa (NYSC) a shekarar 1989/1990.
An gyara hoton (an inganta shi). Asalin hoton yana cikin sashen sharhi (comments).

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un 😭😭Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un😭😭Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un😭😭Hadari Ya F...
25/08/2026

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un 😭😭

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un😭😭

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un😭😭

Hadari Ya Faru Yanzu Hanyar Abuja to Kaduna .

Wadda Akwai Motar KSTA Katsina Wadda Ta Taso Daga Yan ya A Abuja Zuwa Katsina.

Mutane Da Dama Sun Raunata..

Allah Ya Kyauta Gaba, yajikan wadanda s**a rigamu 🙏

Pakistan ta ce an samu gagarumar nasara a tattaunawar da wakilanta s**a yi da shugabannin Iran a Tehran, wadda ta mayar ...
25/08/2026

Pakistan ta ce an samu gagarumar nasara a tattaunawar da wakilanta s**a yi da shugabannin Iran a Tehran, wadda ta mayar da hankali kan hanyoyin samar da zaman lafiya.

Shugaban hafsoshin sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ne ya jagoranci tawagar kasar a ziyarar.

Rahotanni sun ce tattaunawar da ya yi da shugaban Iran da ministan harkokin wajen kasar da kuma shugaban majalisar dokoki ta mayar da hankali ne kan matakan dakile ci gaba da rikicin, da sake bude Mashigar Hormuz, da kuma neman hanyoyin kawo karshen yaƙin da ake yi tsakanin Iran din da Amurka.

An kuma ruwaito cewa Field Marshal Munir ya tuntuɓi Shugaban Amurka, Donald Trump, kafin tafiyarsa Tehran.

Rahotanni sun ce Amurka ta nemi Pakistan ta yi amfani da tasirinta wajen shawo kan Iran ta koma teburin tattaunawa.

Sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa daga Washington game da sak**akon ganawar.

Getty ImagesBayanan hoto,Wani mai bikin Maulidi a birnin Addis Ababa na ƙasar EthiopiaMajalisar kula da lamurran addinin...
25/08/2026

Getty Images
Bayanan hoto,Wani mai bikin Maulidi a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia
Majalisar kula da lamurran addinin Musulunci ta yankin Tigray a ƙasar Ethiopia ta buƙaci Musulman yankin su yi bukukuwan maulidi a cikin gida ko ɗakunan taro, sannan kada su je masallatai sai cikin dare domin gudun hare-hare daga sojojin ƙasar.

“Majalisar ta ce ba za a yi bukin Maulidi a manyan dandalin taruka ba, a maimakon haka za a gudanar da maulidin ne a masallatai, inda za a yi addu’o’i da wa’azi,” a cewar bayanin.

Al’ummar Ethiopia na hutu a yau Talata domin bikin maulidin haihuwar Annabi Muhammad, wanda ke gudana a ƙasashe da dama na duniya.

Majalisar addinin Musuluncin ta yankin Tigray ta ce za a yi bukukuwan na masallatai ne a cikin dare domin gudun hare-haren jirage marasa matuƙa na sojojin gwamnati.

Ana samun rahotannin hare-haren jirage marasa matuƙa a yankin Tigray daga sojojin gwamnatin Habasha, inda irin waɗannan hare-hare s**a faɗa birnin Makelle da wasu sassan yankin, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da raunata fararen hula.

An samu irin wannan hari a ranar 18 ga watan Agusta a birnin na Makelle.

Ethiopia ta dade tana yaƙi da mayaƙan ƙungiyar ƴanta al’ummar Tigray ta TPFL, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da tarwatsa mutane daga muhallansu

An k**a wata tsohuwa wadda hukumomi s**a ce shekarunta 101 a Najeriya bisa zargin sayar da tabar wiwi, wani abu da ya ja...
25/08/2026

An k**a wata tsohuwa wadda hukumomi s**a ce shekarunta 101 a Najeriya bisa zargin sayar da tabar wiwi, wani abu da ya ja hankalin al’umma.

A ranar Asabar ne Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta k**a Esther Ogunmabo, wadda aka ce tana da jikoki, a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya ce an k**a matar ne da “ƙulli-ƙullin wiwi wadda ta kai nauyin giram 90, inda ta ce tana sayarwa ne ga mutunen unguwa”.

NDLEA ta ce matar ta ce ta shiga harkar sayar da ganye ne bayan gobarar da ta lalata shagonta na kayan masarufi. Amma an bayar da belin ta.

Hukumar ta ce wata ƴar tsohuwar ce da ke zaune a birnin Legas ake zargi da tura mata tabar bayan kwana hurhuɗu, inda ita kuma tsohuwar ake zargin tana sayar wa mutane kulli-ƙulli a cikin unguwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa hare-haren Isra'ila na ci gaba da kashe fararen hula a Gaza.Ma'aikatan lafiy...
25/08/2026

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa hare-haren Isra'ila na ci gaba da kashe fararen hula a Gaza.

Ma'aikatan lafiya a yankin sun ce an kashe wata yarinya ƴar shekara 10 da kuma wani yaro ɗan shekara huɗu a cikin kwana ɗaya da ya gabata.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ba ta da masaniya game da kisan yarinyar, inda ma'aikatan lafiya da dangi s**a ce harsashin bindiga ya samu Amal Abu Khater a baya sa'ilin da take zaune tana cin abinci a cikin tantin da take zama da iyalanta a Khan Younis.

Ofishin bayar da agajin jin-ƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce hare-haren Isra'ila sun lalata rumbunan ajiye kaya guda uku mallakinsa a garin Deir al-Balah

Fadar shugaban ƙasar Rasha ta ƙi cewa uffan game da rahotannin da ke cewa wani jirgin jigilar kaya na sojojin Amurka ya ...
25/08/2026

Fadar shugaban ƙasar Rasha ta ƙi cewa uffan game da rahotannin da ke cewa wani jirgin jigilar kaya na sojojin Amurka ya sauka a filin jirgi na Vnukovo da ke birnin Moscow.

Manhajar bibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta FlightRadar ta nuna jirgin na barin sansanin sojin sama na Andrews Airbase da ke jihar Maryland a Amurka sannan ya sauka a Riga, babban birnin ƙasar Latvia, kwana biyu da s**a gabata.

Akwai raɗe-radin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na Rasha cewa ko dai za a yi musayar fursunoni ne ko kuma watakila jirgin ya kai jakadan shugaba Donald Trump ne domin tattaunawa kan Ukraine.

A baya akwai rahotannin da ke cewa jakadan Trump, Steve Witkoff da Jared Kushner za su iya halartar bikin ranar ƴanci ranar Litinin a birnin Kyiv, sai dai ba a ga hakan ba.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when labarai da rahotanni posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share