09/08/2026
RUNDUNAR TSARO TA K**A WATA MATASHIYA KAN YUNKURIN SATAR JARIRI A KADUNA
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar cafke wata matashiya budurwa cikin tsakiyar dare, bayan an gano ta da shirin garkuwa da sace wani sabon jinjiri daga wani babban asibiti da ke jihar.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, wasu maza da ake zargi suna tare da matashiyar sun tsere da gudu nan take bayan da jami'an tsaro s**a gano lamarin.
Haka kuma, ana gudanar da bincike mai zurfi kan zargin cewa akwai yiwuwar hadin baki da daya daga cikin ma'aikatan asibitin domin gudanar da wannan danyen aiki cikin sauki.
A yayin binciken, jami'ai sun yi kokarin kiran lambobin wayoyin mutanen da s**a tsere, sai dai sun ki daga kiran kuma daga baya s**a kashe wayoyin baki daya don boye sawunsu.
Yayin da ake gudanar da binciken farko, wadda ake zargin ta ce ba ta san da nufin satar jaririn ba. Ta bayyana cewa mutanen da s**a tsere ne s**a umarce ta da ta dauko jaririn, da nufin za a kai shi wani wuri na musamman don ba shi taimako da sadaka.
Sai dai, sauran bayanan sun nuna cewa tana da cikakkiyar masaniya kan dukkan tsarin. Ita kuma ta ci gaba da jaddada cewa wadanda s**a gudu din sune ainihin jagororin tafiyar kuma su kadai s**a san gaskiyar lamarin.
Rundunar tsaro ta bayyana cewa an tsananta bincike domin gano inda sauran mutanen da s**a tsere suke, da kuma bankado babban dalilin da ya sa suke son sace jaririn.
Haka zalika, asibitin ya dauki matakan tsaro na ninka jami'ai domin tabbatar da lafiyar jarirai da iyayensu.
📷 HR Reporters
✓Follow, Share, And Subscribe =>