27/04/2025
cNGN Stablecoin: Nijeriya Tace Baza'a Barta a Baya Ba.
Kwanakin baya nayi bayani akan menene stablecoins da yanda suke aiki, har ma na bayarda misali da stablecoins da muka fi sani wato USDT da USDC wayanda s**a samu sahalewar babban bankin Amerika.
cNGN stablecoin ne da akayi pe***ng dinsa da Naira, wato kamar yanda USDT take daidai da daraja Dollar Amerika haka cNGN stablecoin yake daidai da darajar Naira dake aljihunmu da bankunan mu. cNGN sun samu sahalewar gwamnatin Nijeriya, kuma a yanzu haka har an fara trading da cNGN a wasu kasuwanin crypto irin Busha da Quidax. Yanzu haka achikin wayannan kasuwani zaku sayi duk coin din da kuke so da cNGN kamar yanda muke saya da USDT. Misali, kamar yanda muke da USDT pair kamar BTC/USDT, ETH/USDT, SOL/USDT da sauransu, haka zamu ga BTC/cNGN, ETH/cNGN, SOL/cNGN da sauransu.
Da cNGN stablecoin kun huta da matsalar scammers ko bata lokachi a P2P, domin kuwa babu ruwanku da yin P2P idan zaku chire kudinku daga kasuwa indai akwai cNGN a exchange da kuke amfani da ita, domin kuwa kai tsaye zaku tura cNGN daga daga exchange dinku zuwa bankinku kudin suje babu bata lokachi. Haka zalika idan zaku saka kudi an exchange domin yin sayen coin babu ruwanku da yin P2P domin kai tsaye zaku tura kudi daga bankinku zuwa exchange. Idan kun tura cNGN zuwa bankinku zasuje ne a matsayin normal kudi kamar wani ya tura maku, haka zalika idan kuka tura kudi daga bankinku zuwa exchange zasuje ne amatsayin cNGN babu bukatar conversion. Kamar yanda nace a yanzu kasuwannin Busha da Quidax ne kadai s**a dora cNGN amma ana tattaunawa da wasu kasuwannin domin suma su dora cNGN. Kuma a hankali nan gaba cNGN zata hau kan dukkan kasuwannin crypto da muke amfani dasu kamar irinsu Bitget, Roqqu, Kucoin, Bybit, MEXC da sauransu yanzu ana nan ana tattaunawa da Bybit da MEXC. Sannan zamu dinga sayen coins kai tsaye da cNGN dinmu ba tareda bukatar USDT ba.
Babban kamfanin blockchain dake Nijeriya wato Convexity mallakin Sir Adedeji Owonibi da hadin gwiwar manyan blockchain projects irinsu Interstellar da Alpha Geeks sune s**a samar da cNGN. Yanzu haka cNGN tana kan manyan blockchains irinsu Ethereum, Binance Smart Chain (BSC), Bantu, Tron, Base, Polygon da Assetchain.
Copied from mentor.
Sunusi Danjuma Ali
Founder, SCTv Africa II Content Creator II Marketer II Web3 Advocate.