28/05/2024
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Naso In Magana Ne Dangane Da Wannan Musiba Da Ta Same Mu A Daidai Wannan Lokaci, Na Rashin Wadannan Bayin Allah, Shugaban
Kasar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, Ayatullah Sayyid Ibraheem Ra’isi, Da Wazirin Sa Na Harkokin Waje, Husain Amir Abdullahian, Da
Limamin Tabriz Kuma Wakilin Sayyid Qa’id A Lardin Gabashin Azerbaijan, Da Gwamnan Tabriz, Da Wadansu Wanda Suke Tare Da Su.
A Abinda Zamu Iya Ce Mishi Wani Hadisa (Wani Abinda Ya Faru) Mummuna Da Ya Auku A Helikoftan Da Suke Tafe Wanda Aka Rasa
Su Gaba Dayan Su. Wannan Ya Auku A Daidai Lokacin Da Muke Cikin Bikin Tunawa Da Ranar Haihuwar Imam Ridha (A.S), Ranar 11
Ga Watan Zulqa’ada.
Muna Cikin Wannan Biki Sai Kawai Labari Ya Zo Mana Cewa Ainihin Ga Halin Da Ake Ciki, Ba’a Ga Jirgin Shugaban
Kasa1 Ba (Na Iran)!, To Wannan Sai Yasa Ainihin Wannan Zama Namu Na Biki Ya Koma Jaje, Aka Fara Kuma Ana Addu’o’i, Wanda Mu
Anan Hakannan Aka Yi Ta Addu’o’i, Muka Yi Ta Bin Abubuwan Da Ke Faruwa Dakika Bayan Dakika, Ainihin Idanun Mu Basu Iya Bacci
Ba A Wannan Dare.
Haka Zalika Kuma Dukkan Sassa Na Duniya, Ainihin Musamman Anan Haramin Imam Ridha (A.S) Wanda Shima Taron Mutane Masu Dinbin Yawan Gaske S**a Koma Addu’o’i, Na Bidan Fatan Mafita Garesu. Haka Ma Ainihin Yan’Uwan Da S**a Tafi
Hajji Suma S**a Yi Dafifi A Haramin Makka Da Madina Duk Suna Ta Addu’o’i, To Hakanan Muka Kwana Bamu Yi Bacci Ba!, Muna
Taraqqubin (Jiran) Me Zamu Ji?,
Saboda A Lokacin Ana Cewa Hadari Da Iska Da Ruwan Sama Ya Hana Ainihin Masu Kokarin Isa Wurin
Don Ceto Su, Ainihin Basu Iya Isa Wurin Ba, Har Saida Wayewan Gari!, Sannan Kuma Daga Karshe Aka Isa, Ainihin Labari Mara Dadi
Ya Iso Mana, Cewa Ainihin Ba’a Samu Ko Dayan Su Da Rai Ba. Wannan Ya Kada Mu Sosai, Ya Girgiza Mu Sosai, Ya Samu Cikin
Matsanancin Bakin-Ciki Da Dimuwa!, Mun Girgiza Sosai, Kuma Kalmomi Ba Zasu Iya Bayyana Irin Kaduwar Mu Da Alhinin (Jaje) Mu
Da Bakin-Cikinmu A Wannan Rana Ba.
_Jagora Sayyid Zakzaky Hafizahullah
أَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ أَنْ تُصَلِّيَ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وآلِ مُحَمَّدٍ وَأَنْ تَأْتِيَ قَائِدَنَا إِبْرَاهِيمَ زَكْزَكِي بِفَرَجٍ مِنْ عِنْدِكَ يُشْبِهُ حُسْنَ ظَنِّهِ بِكَ يَا أَرْحَمَ الرَّاحِمِين.