11/08/2025
Fargaba Bayan Kwashen Sojoji Daga Tashar Bawa a Karamar Hukumar
Rahotanni daga Karamar Hukumar Sabuwa, Jihar Katsina, sun tabbatar da cewa an kwashe jami’an tsaro daga Tashar Bawa, lamarin da ya haifar da firgici tare da sa wasu mazauna yankin fara barin gidajensu domin neman mafaka.
Tashar Bawa, wadda ke iyaka da Jihar Kaduna, na cikin yankunan da s**a dade suna fama da hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da kuma rasa rayuka, abin da ya tilasta wa wasu mazauna yin hijira. A baya, bayan kafa sansanin sojoji a yankin, rahotanni sun nuna raguwar hare-haren da kusan kaso 90 cikin ɗari, kamar yadda wasu mazauna s**a shaida wa Katsina Times.
Sai dai a safiyar Asabar, mazauna s**a wayi gari da ganin an kwashe dukan sojojin daga yankin ba tare da sanin dalili ba. Wannan mataki ya tayar da hankulan jama’a, inda wasu s**a fara kwashe kayayyakinsu don komawa wuraren da s**a fi samun tsaro.
Wasu mazauna sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da hukumomin tsaro da su gaggauta dawo da jami’an tsaro a yankin, musamman ganin mafi yawan mazauna manoma ne, kuma a halin yanzu ana tsakiyar damina, lokaci mai muhimmanci ga aikin gona.
Source:katsina city News page
Dr. Dikko Umaru Radda