Hisnul muslims

Hisnul muslims Wannan page din munbudeshine don taimakama kanmu wajen koyan addu'o'i cikin sauki, daga Qur'ani da su

Zaka iya zuwa  duniya karayu tsawon shekara 40, 60, 70, 80, 90, 100, ko sama da haka,  kwanciyar kabari  kuwa  kana iya ...
25/09/2024

Zaka iya zuwa duniya karayu tsawon shekara 40, 60, 70, 80, 90, 100, ko sama da haka,

kwanciyar kabari kuwa kana iya shafe sama da shekara 200, 300, 400, 500, ba'ayi tashin alkiyama ba.

"Kuma a nan duniya akeso kayi tanadin wancan doguwar kwanciyar"

A cikin shekara 40, 60, 70, 90 duk mai tunani ba za'i shagala da duniya akan ibada ba.
"Allah yasa mucika da imani"

24/09/2024

MAINENE WAYEWA?

1. Wayewa shi ne ka riƙe addinin ka da kyau.
2. Wayewa shi ne ka rike al'adun ka masu kyau.
3. Wayewa shi ne ka gane alkhairi ka aikata shi, kuma ka gane sharri ka guje shi.
4. Wayewa shi ne ka haɗa neman duniya da lahira, domin duniyar ka ta yi kyau, haka lahirar ka.
5. Wayewa shi ne ka zama mai kishin ƙasar ka da al'ummar ka.
6. Wayewa shi ne ka gane masoyinka da maƙiyin ka kuma ka iya zama da kowa.
7. Wayewa shi ne ka yiwa kanka shiri, domin ajiya maganin wata rana.
8. Wayewa shi ne ka iya aje komai inda ya dace, sanda ya dace, kamar yadda ya dace.
9. Wayewa shi ne ka auna magana kafin ka faɗe ta, ka zo kana nadama .
10. Wayewa shi ne Kasan za a mutu, kuma za a gamu da Allah, kuma zai yi hisabi, don haka ka fara yiwa kanka tun daga nan duniya .
11. Wayewa Shi ne ka rayu idan za ka iya, ba cuta ba cutarwa, kuma kada kayi abin kunya da zai dame ka nan gaba.
12. Wayewa shi ne ka yadda da yadda Allah ya yi ka, Kada ka rena kanka da baiwar da Allah ya yi maka.

Wannan shine ake kira da rayuwar fa tun bakasan waye kaiba har kazo kasan waye kai daga karshe sunanka zai bace daga bak...
17/09/2024

Wannan shine ake kira da rayuwar fa tun bakasan waye kaiba har kazo kasan waye kai daga karshe sunanka zai bace daga bakunan mutane saboda yanzu Babu Kai araye da can anayi da Kaine alokacin da kananan Amma yanzu ba dakai akeyiba, Kai duniya runfar Kara

Muna rokon Allah ya sa muyi kyakykyawan karshe.

Ameen
17/09/2024

Ameen

02/09/2024

ALLAH YA JIKAN MU:

Duk Kofar da ka ganta a rufe to tana da mabudi.. Kada ka saki baki kana jiran ta bude da kanta!!

Komai a duniya yanada mabudi.. Mabudin Ilimi shine tambaya.. Mabudin nasara hakuri,, mabudin arziki tsoron ALLAH,, Mabudin zaman lafiya adalci da Gaskiya!!

Babban mabudin Alkhairi shine istigfari. Idan kana yawaita shi matsalolinka za su kau,, Damuwarka zata gushe.. sauki daga UBANGIJI zai zo maka!!

Sadaka da Addu'a sune maganin masifa da fadawa mummunar qaddara. Ana fatan mutumin kirki a kullum ya tabbatar yayi Sadaka yayi Addu'a. Allah ya amsa mana, amin

YA ALLAH Ka gafarta mana ka kawo mana sauki acikin rayuwar mu na yau da kullum, Ameen.

02/09/2024

1. Mafi girman haske, ilmi
2. Mafi girman duhu, jahilci
3. Mafi girman kyauta, afuwa
4. Mafi munin zance, karya
5. Mafi kyawun zance, gaskiya
6. Mafi kusantuwar al'amari, tashin al'qiyama
7. Mafi girman arziki, wadatar zuciya
8. Mafi kyawun hali, kunya
9. Mafi munin hali, kisan kai
10. Mafi kusantar ALLAH, ibada
11. Mafi kusantar shedan, hassada
12. Mafi kusantar aljanna, ciyarwa
13. Mafi kusantar wuta, rowa.
14. Allah ya kiyaye mu da Son Xuciya Ameen.

Please share Don wasu su anfana Allah a bamu ladan.

8 powerful Du’as that work like a miracle.
12/07/2024

8 powerful Du’as that work like a miracle.

12/07/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! Hamman Yero Goggo Manma, Zainab Sabiu Zainab Sabiu, Yusuf Kasim, Musbahu Ibrahim Halilu, Suleiman Adamu, Maman Ihsan, Rukayya Tureta, Ishaque Gani, Mamta Humaira, Zainab Sani, Khadeejah Sanee, Iliyasu Hauwa MJ, Hajara Abdurrahma, Amina Haruna, Sulaiman Ibrahim Yaro, Loukman Adamou, Seifullahi Good Ibrahim, Yahya Usman Abubakar, Ameena Ahmad, Khadija Abdullahi, Sunusi Ahmed Sino, Abbas Ibrahim, Aisha A Tahir, Salisu Konofari, Aminu Ibrahim, Nana Fuwaida Muhammad

04/07/2024

عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ عَنِ النَّبِيِّ ﷺ قَالَ: «مَنْ تَعَارَّ مِنَ اللَّيْلِ، فَقَالَ: لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، الحَمْدُ لِلَّهِ، وَسُبْحَانَ اللَّهِ، وَلاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ، ثُمَّ قَالَ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي، أَوْ دَعَا، اسْتُجِيبَ لَهُ، فَإِنْ تَوَضَّأَ وَصَلَّى قُبِلَتْ صَلاَتُهُ»

Narrated ʿUbādah bin aṣ-Ṣāmit The Prophet ﷺ said: "Whoever gets up in the night and says: Lā ilāha ill-Allāhu waḥdahu lā sharīka lahu, lahul-Mulku walahul-Ḥamdu wa huwa ʿalā kulli shayʾin qadīr, al-Ḥamdulillāh, wa SubḥānAllāh, wa Lā ilāha ill-Allāh, wAllāhu Akbar, wa lā hawla wa lā quwwata illā billāh. (None has the right to be worshipped but Allāh. He is the Only One Who has no partners, His is the kingdom and all the praises are for Him, He is Omnipotent. All the praises are for Allāh. All the glories are for Allāh. And none has the right to be worshipped but Allāh, and Allāh is the Most Great and there is neither might nor power except with Allāh). And then says: 'Allāhummaghfirlī' (O Allāh! Forgive me), or invokes (Allāh), he will be responded to and if he performs ablution and prays, his Ṣalāh will be accepted."

Ubadah bn as-Sāmit ya ruwaito cewa, Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya tashi a cikin dare, ya ce: “Lā ilāha ill-Allāhu waḥdahu lā shariika lahu, lahul-Mulku walahul-Ḥamdu wa huwa ‘alā kulli shay-in Qadīr, Subhanallah ,walhamdulillah wa Lā ilāha ill-Allah, wAllāhu Akbar, wa lā hawla wa lā quwwata illā billāh. Gõdiya ta tabbata ga Allah, kuma bãbu wani abin bautãwa fãce Allah. Sa'an nan kuma ya ce: 'Allāhummaghfirli' (Ya Allah! Ka gafarta mini), ko kuma ya yi addu'a ya kira (Allah), za a amsa masa, kuma idan ya yi alwala ya yi addu'a, za a karɓi sallarsa.

Ya Allah! Ka amshi addu'oinmu kasanya mana albarka arayuwarmu.

Allah kasa mu cika da imani ka bamu ikon tashi dashi.
03/07/2024

Allah kasa mu cika da imani ka bamu ikon tashi dashi.

02/07/2024
Ya Allah karka azabtar da mu in munyi mantuwa kuma karka K**a mu in mun Saba maka!  Hisnul muslim✍️
02/07/2024

Ya Allah karka azabtar da mu in munyi mantuwa kuma karka K**a mu in mun Saba maka!

Hisnul muslim✍️

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisnul muslims posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category