18/02/2025
Ƴansanda na neman mawaki Portable bisa kai wa ma'aikatan gwamnatin Ogun hari
Rundunar ƴanandan jihar Ogun ta bayyana cewa tana neman mawakin nan mai suna Habeeb Olalomi, wanda aka fi sani da Portable ruwa a jallo bisa zarginsa da jagorantar wani hari akan jami’an gwamnati da ke gudanar da ayyukansu a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola ya fitar a jiya Litinin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 10:00 na safe lokacin da jami’ai uku daga ma’aikatar tsare-tsare da raya birane ta jihar Ogun, Onabanjo Abidemi, Raymond Lateef -Ridwan a Oke-Osa, Tigbo Ilu Ota.
A yayin aikin, sai jami’an su ka je wajen wani dattijo, wanda daga baya aka bayyana shi a matsayin mahaifin Portable, a mashaya a Odogwu, inda aka ce wajen na mawakin ne
Bayan gabatar da kansu kuma s**a nemi a basu takardun ginin su gani, sai mahaifin Portable din ya sanar da su cewa ba sa hannun sa kuma ɗan nasa baya nan.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa duk da haka, bayan ɗan lokaci,bsai Portable, ya jagoranci matasa su tara dauke da muggan mak**ai, su ka kai hari kan jami'an.
An ce jami’an sun samu raunuka daban-daban amma sun yi nasarar tserewa inda s**a kai rahoton harin ga ofishin ‘yansandan yankin Ita.
Yayin da aka k**a mutane tara daga cikin yaran na Portable, mawakin ya gudu daga wurin kuma tun a lokacin ya buya.
Daily Nigerian Hausa