
31/08/2025
Ban taɓa sanin cewa next of kin baƙar wahala yake sha kafin ya fito da kuɗin mamaci daga banki ba, sai da wani amininmu ya yi mana sharing information ɗin a shekarar da ta gabata.
Yawancinmu mun zaci in dai kai ne next of kin to da zarar wanda ya rattaba sunanka ya rasu to kawai kana zuwa banki kudinsa zasu ɗebo su baka, to ba haka sha’anin yake ba
Idan mutum ya faɗi ya mutu to ku sani Next Of Kin bai da ikon taɓa kuɗin mamacin, sai an bi wasu dogayen ƙa’idoji masu cin ran tsiya, musamman idan babu rubutu.
Akwai abin da banki ke kira ‘Legal Probate. Wani tsari ne mai ɗaukar lokaci mai tsawo da cin rai da cacar kuɗi kafin a tabbatar da wane ne zai mallaki kuɗin da mamaci ya mutu ya bari. A ƙarshe idan kuɗin sun fito, sai an yi musu giɓi wajen biyan Legal fee, su ma kuɗi ne masu yawa.
Akwai hanya ɗaya da mutum zai iya kaucewa wannan matsalar, hanyar ita ce:- ka buƙaci bankinka su baka form mai suna B.O.D. ma’anarsa da turanci ita ce Payable On Death. Wato a biya yayin da ka mutu.
Wannan form ɗin shi ke ɗauke da sunan waɗanda zasu gaje mutum. Abin kawai da magada suke buƙata shi ne su nuna abin da ake kira Death Certificate.
Yin amfani da form ɗin B.O.D. ne kaɗai ke iya warware matsalar banki su riƙe kuɗin mamaci tsawon lokaci kafin ya je hannun magada.
Copied