06/11/2025
ALLAH YA ISA! BANDITS SUN CUTAR DA AL’UMMAR FULANI
Allah ya Isa! Wannan kalma ce kawai zamu iya furtawa tsakaninmu da waɗannan yan bandits din da s**a cutar da al’ummarmu ta Fulani fiye da yadda kalmomi zasu iya bayyanawa.
Sun raba da yawa daga cikinmu da dukiyoyinsu, s**a mai dasu talakawa bayan sun taɓa zama masu arziki da daraja.
Sun raba da yawa daga cikinmu da gidajensu da ƙasarsu, s**a tilasta musu yin hijira zuwa makobtan kasashe ko wasu jihohi cikin ƙasƙanci, tsoro da wahala.
Sun bata mana suna gaba ɗaya a idon jama’a, har ta kai ga cewa a wasu wurare, da zarar ka ambaci kalmar “Fulani”, mutane na iya shiga cikin tsoro, su gudu ko su ɓoye, alhali ba kowane ɗan Fulani ne mai laifi ko dan ta'adda ba.
Yanzu al’ummar Fulani sun zama abin tsangwama da wariya a ko’ina; sun zama abin gudu da kyama, k**ar ba ‘yan Adam ba. Wannan abu yana da matuƙar ciwo da takaici, domin ya lalata mutuncin kabilar da aka sani da gaskiya, mutunci, da halin kirki tun fil azal.
Wannan babban zalunci ne da ya haifar da ciwon rai da zubar da mutunci ga al’umma mai tarihi da ɗabi’a irin ta Fulani.
Mutanenmu da aka sani da gaskiya, amana, tausayi da karamci, yanzu an mai dasu k**ar basu da daraja, saboda wasu ‘yan ta’adda da s**a ɓata masu suna.
Ina kira ga Gwamnatin Tarayya, ta Jihohi, da Sarakunanmu na gargajiya dasu tsaya tsayin daka wajen ganin an dawo da mutuncin Fulani, an ware masu gaskiya daga ‘yan ta’adda, kuma a taimaka wa waɗanda s**a rasa komai sanadiyyar wannan masifa.
Haka kuma muna kira da Gwamnati ta ɗauki mataki mai ƙarfi da ya dace akan waɗannan bandits din, domin a kawo ƙarshen zalunci da barna da suke yi wa al’umma.
Muna kuma roƙon kungiyoyin agaji, religious bodies, da masu hannu da shuni, dasu kai taimako ga waɗanda aka zalunta, koda da kayan sawa ne, kayan abinci, da kulawa, domin su san cewa an damu dasu, an san halinda suke ciki.
A matsayinmu na yan Adam, muma muna da haƙƙi na rayuwa cikin aminci da mutunci k**ar kowa. Kada mu bar wasu ‘yan tsiraru su bata mana suna, su kuma hallaka mana al’umma.
A ƙarshe, muna roƙon Allah Madaukakin sarki ya kawo mana zaman lafiya, Ya tsarkake sunanmu daga abin da bamu da hannu a ciki, Ya kuma dawo mana da mutuncinmu da martabar da muka rasa.
Allah ya kare Fulani, ya kare al’ummar Najeriya baki ɗaya daga fitina, zalunci da tsanantawa.
✍️ Muhammad Khalid Hussaini
(De General)
06/11/2025