06/08/2025
                                            TAKARDAR KORAFI ZUWA GA GWAMNATIN JIHAR BAUCHI...
TA HANNUN MAI GIRMA KWAMISHINAN MA'AIKATAR ILIMI MAI GIRMA DA (Ministry of Higher Education and Regional Integration)
TAKARDAR KORAFI AKAN RASHIN KARBO TAKARDUN SHAIDA (CERTIFICATES) NA DALIBAN DA S**A GAMA A AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, TA HANNUN SHUGABAN A.D. RUFA’I COLLEGE OF EDUCATION, LEGAL AND GENERAL STUDIES, MISAU.
Assalamu Alaikum.
Mu ne mambobin ƙungiyar dalibai masu karatun fannin Shari’a a Kwalejin Ilimi, Doka da Karatun Bai Daya da ke Misau, Jihar Bauchi.
Muna rubuto wannan takarda ne domin mu shigar da ƙorafi dangane da rashin karɓo takardun shaidar kammala karatun mu (original certificates) na shekarar 2019/2024 daga jami’ar Ahmadu Bello University (ABU) Zaria.
Wadannan takardu ne kawai za su ba mu damar ci gaba da karatu a manyan jami’o’in Najeriya, kamar yadda hukumar JAMB ta tanadar.
Sai dai har yanzu a wajen mu muna kallon shugabancin makarantar bai yi wani yunkuri na karbo takardun ba.
Mun fahimci cewa takardun sun makale ne saboda rashin biyan kudin da ABU ke bukata na accreditation, affiliation, da kuma kudin takardun shaida.
Shugabancin makarantar yana mai nuna mana cewa gwamnati ce bata bayar da kudin ba, alhali kuwa mu dalibai mun biya miliyoyin kudade na rajista, kuma mun gudanar da bincike wanda ya nuna cewa gwamnati ta riga ta bayar da nata kaso.
Mun kuma yi ƙoƙarin haɗa kuɗi da kanmu don a wakilta mu zuwa Zaria domin karbo takardun, amma sai muka fuskanci barazana daga hukumar makarantar.
Muna zargin Makarantar ta fara amfani da wasu daga cikin mu a sirrance don hana ci gaban wannan yunkuri.
Wannan ya nuna cewa ci gaban ilimin mu bai zama babban abin da shugabancin makarantar ke mayar da hankali a kai ba.
Wannan shine dalilin da ya sa muka zo ofishin Mai Girma Kwamishiniya domin mika koken mu tare da fatan cewa gwamnati za ta kawo mana dauki, ta share mana hawaye, domin mu samu damar ci gaba da karatun mu.
Mun yi imanin cewa hakan zai taimaka gaya wajen bunkasa harkar ilimi da ci gaban al’ummar Jihar Bauchi.
Muna fatan samun kulawa da saurin daukar mataki a kan wannan matsala.
Na gode da kulawarku.
Mai Shigar da Kuka:
Nuraini (a madadin daliban fannin Shari’a)