Hausa24

Hausa24 HAUSA24, Za Ta Kasance Wata Kafar Yada Labarai Da Za Take Kawo Muku Labarai Da Dumi-Dumin Su, Cikin Harshen Hausa!

Fagen harkar yada labarai fage ne mai fadin gaske, da dama sun zo sun tafi bayan sunyi abinda s**a yi, wasu ma sun zo basu yi komai ba sun tafi ba tare da ko labarinsu an ji ba. Mun sani kuma mun aminta igiya biyu ce kadai za ta iya rike mu, har mu ma muyi abinda muka yi. Wadannan igiyoyi su ne: GASKIYA da GOYON BAYANKU, za mu rayuwa idan har akwai wadannan igiyoyi. H24 za ta zamo wata takar yakin

Hausawa ‘yan Nijeriya, domin yakar karya da kare gaskiya a kodayaushe, koda kuwa a hannu masu mulki ne. Ta haka ne kadai za mu cimma burinmu da naku baki daya.

Innalillahi Wa'ainna Ilaihi Raji'un..Allah yayi wa tsohon shugaban ƙasar Nigeria Gen. Muhammadu Buhari rasu yau a Birnin...
13/07/2025

Innalillahi Wa'ainna Ilaihi Raji'un..

Allah yayi wa tsohon shugaban ƙasar Nigeria Gen. Muhammadu Buhari rasu yau a Birnin London bayan fama da jinya.

Iyalan shugaba Buhari sun tabbatar da haka a yammacin wannan rana ta Lahadi.

13/07/2025

Innalillahi Wa'ainna Ilaihi Raji'un..

Allah yayi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari rasu yau a Birnjn London bayan fama da jinya.

ME KE FARUWA NE: Duka jiga-jigan Kano da Arewacin Najeriya sun hallara a Madina domin halartar Janaizar margayi Aminu Al...
01/07/2025

ME KE FARUWA NE: Duka jiga-jigan Kano da Arewacin Najeriya sun hallara a Madina domin halartar Janaizar margayi Aminu Alhassan Dantata

Amma jama’a nata tambaya ina Madugu, har yanzu ba a ga hotonsa a wajen ba...

AREWACIN NAJERIYA YA SAMI KARIN MEGA WAT 120 NA WUTAR LANTARKIKamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya, TCN, ya sanar...
01/07/2025

AREWACIN NAJERIYA YA SAMI KARIN MEGA WAT 120 NA WUTAR LANTARKI

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya, TCN, ya sanar da samar da wutar lantarki da sabbin taransfoma guda biyu da aka girka a tashar wutar lantarki mai karfin kilovolt 330/132/33 da ke Birnin Kebbin jihar Kebbi.

Kamfanin ya fitar da sanarwar ne a ranar juma'ar 27 ga watan Yuni, 2025.

A yanzu ƙarfin wutar da tashar ke samarwa ya tashi daga 300 MVA zuwa 450 MVA. Hakan na nufin kamfanin zai rika bai wa rumbun rarraba wutar lantarki da ke Kaduna ƙarin wutar lantarki har na Mega Wat 120 domin raba wa jihohi irin su Kebbi, Sokoto da kewaye.

Bugu da ƙari kamfanin ya sami damar ci gaba da samar da wutar lantarki a babban birnin Yamai ta Jamhuriyar Nijar wanda a kwanaki kafofin labarai s**a ruwaito tana fama da rashin wadatacciyar wutar lantarki.

Wannan nasara ta biyo bayan jajircewar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin cewa Najeriya ta fita daga ƙangin rashin wutar lantarki, wanda an sha jiyo shi ya na nanata yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan samar da ababen more rayuwa a ƙasar wanda wutar lantarki da hanyoyi ke kan gaba a cikin ajandodinsa.

Innalillahi Wa'ainna Ilaihi Raji'un.Al'ummar Jihar Kano, Manyan Nigeria dama na 'ƴan kasa baki daya naci gaba da alhinin...
28/06/2025

Innalillahi Wa'ainna Ilaihi Raji'un.

Al'ummar Jihar Kano, Manyan Nigeria dama na 'ƴan kasa baki daya naci gaba da alhinin rashin Babban dan kasuwar Jihar Kano kuma dattijo mai fada a Kano dama kasa Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Alhaji Alhasan Dantata, ya rasu a daren jiya a kasar Haddaiyar daular Larabawa (UAE) yayin da za'a binne shi a kasar saudia kamar yadda yabar wasiya ga Iyalan sa. Allah ya karbi rayuwarsa yana shekaru 94 a Duniya.

Allah ya gafarta masa yasa aljannah makoma

CIGIYA: INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN !!!An sace mota ta a Shoprite Kaduna don Allah ku tayani cigiya ta hanyar "shar...
28/06/2025

CIGIYA: INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN !!!

An sace mota ta a Shoprite Kaduna don Allah ku tayani cigiya ta hanyar "sharing"

Bayani akan motar wacce aka sace a Shoprite Kaduna:

⚫️2007 VIBE PONTIAC

⚫️ Fara ce

⚫️ Lambar motar: DKA-549CKJ (Kaduna)

CHASIS NUMBER: 5Y2SM62843Z475945

Idan Allah yasa an dace a kira ni a : IBRAHIM SHEHU 0803453054 ko kuma a sanar da duk wani ofishin yan sanda mafi kusa! Allah yasa a dace!

Matasa sun ƙona wani babur ɗin Adaidaita sahu da ake zargin masu kwacen waya ne akan titin Tarauni zuwa gidan gwamnati.A...
21/06/2025

Matasa sun ƙona wani babur ɗin Adaidaita sahu da ake zargin masu kwacen waya ne akan titin Tarauni zuwa gidan gwamnati.

Arewa Updates ta rawaito.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da yake duba waɗanda harin ƴan bindiga ya rutsa da su a jihar Benue a yau.
18/06/2025

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da yake duba waɗanda harin ƴan bindiga ya rutsa da su a jihar Benue a yau.

Najeriya Ba Za Ta Zama Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya Ba – Shugaba TinubuShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai ...
12/06/2025

Najeriya Ba Za Ta Zama Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya Ba – Shugaba Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai bari Najeriya ta koma ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba a zamaninsa.

Yayin da yake jawabi ga zaman haɗaka a Majalisar Tarayya a ranar Alhamis domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya kore raɗe-raɗin da ƴan jam’iyyun adawa ke yi na iƙirarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Yayin da yake bada amsa kan tsoron yan adawa na yadda ake tururwae dawowa jam’iyyar APC, Shugaba Tinubu ya ce jam’iyyar APC za ta aikata “babban kuskuren siyasa” idan ta hana ’yan jam’iyyun adawa shigowa cikin jam’iyyar.

Ya ce, “Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba. Wannan ba zai faru ba. Amma za mu aikata laifin siyasa idan muka rufe ƙofofin ga waɗanda ke son shiga APC.”

Idan ba a manta ba, manyan yan adawar Gwamnatin Shugaba Tinubu sun cika kafafen yaɗa labarai da cewa ana ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya daya, lamarin da Gwamnatin ta bayyana a matsayin ruɗewar yan adawa duba da yadda suke rasa mabiya suna dawowa jam’iyyar APC.

A kwana-kwanan nan an samu dawowar Gwamnoni masu ci, Yan Majalisun Dokoki da Majalisar Dattawa daga sassa daba daban na ƙasar zuwa Jam’iyyar APC daga wasu jam’iyyun adawa dake ƙasar.

05/06/2025

Miliyoyin Mahajjata daga sassa na duniya ke gabatar da ibadar aikin hajjin Bana kasancewar yau ake gudanar da babban rukuni cikin rukunonin aikin aikin Hajji wato ranar Arfa a kasar saudiya.

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta'aziyyar Mutanen Da S**a Rasu A Ambaliyar Garin MokwaGwamnatin Tarayya ta bayyana alhini bisa ...
31/05/2025

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta'aziyyar Mutanen Da S**a Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa

Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhini bisa ambaliyar da ta auka wa garin Mokwa a Jihar Neja, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba ɗaruruwan jama'a da muhallan su.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu cikakken bayani kan halin da ake ciki kan wannan ibtila'in, kuma ya umurci dukkan hukumomin agaji da na tsaro da su ƙara zage dantse wajen gudanar da ayyukan ceto da agaji.

Ya ce: “Tunani da addu’o’in mu suna tare da iyalan da s**a rasa 'yan'uwan su da kuma duk waɗanda ambaliyar ta shafa.”

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da haɗin gwiwar Sojojin Nijeriya da Gwamnatin Jihar Neja suna aiki ba dare ba rana wajen kai ɗauki ga waɗanda abin ya shafa.

Gwamnatin Tarayya ta yaba da jarunta da sadaukarwar jami’an farko da masu aikin sa kai da ke ci gaba da sanya rayuwar su cikin haɗari don ceton wasu.

Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa.

A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda s**a rasu, tare da jaddada cewa al'ummar ƙasar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa wajen tallafa masu ba.

*TSOHON SHUGABAN ƘASA BUHARI YA YABA WA SHUGABAN ƘASA TINUBU* Tsohon shugaban Najeriya, *Muhammadu Buhari* , ya taya shu...
28/05/2025

*TSOHON SHUGABAN ƘASA BUHARI YA YABA WA SHUGABAN ƘASA TINUBU*

Tsohon shugaban Najeriya, *Muhammadu Buhari* , ya taya shugaban ƙasa *Bola Ahmed Tinubu* murnar cika shekaru biyu a kan mulki, tare da cewa kamar yadda jam’iyya da gwamnati ke murna, ya kuma kamata ƴan ƙasa su tuna cewa shugabanci tafiya ce marar iyaka.

Buhari ya kuma ya kira da a ci gaba da mara wa gwamnatin APC baya domin sauyi ba ya samuwa nan take, dole sai sannu a hankali.

Ya kuma yaba da irin ƙoƙarin da gwamnatin ke yi wajen magance matsalolin talauci da tsadar rayuwa, sannan kuma ya ƙara da cewa ka da a bar alhakin shawo kan matsalar kacokam a kan gwamnati, dan haka ya zama wajibi kamfanoni masu zaman kansu da sauran ƴan ƙasa su ma su ba da tasu gudunmawar ta duk hanyar da za su iya.

Ya kuma ƙara da kira ga ƴan Najeriya da su ƙarfafa imaninsu kan samun kykkyawar gobe a ƙasar nan.

Signed:
Garba Shehu
28 May 2025

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa24:

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share