
26/07/2025
AC MAIWADA: Matashin Bakatsinen Da Ya Shahara A Fannin Hulɗa Da Jama'a A Harkokin Gwamnati
Daga Muhammad Bashir, Muhammad Aliyu Rimaye
A kaf taron matasan da ke aiki a ma’aikatun gwamnati a yanzu—musamman a hukumomin tsaro—sa'annan suke taka muhimmiyar rawa a fannin bunƙasa martabar hukumomin, ba yadda za a yi; a kasa ambaton sunan Assistant Comptroller of Customs Abdullahi Aliyu Maiwada, wanda a halin yanzu shi ne Jami'in Hulɗa da Jama'a na Ƙasa (National PRO) a Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS).
AC Maiwada, wanda ko shekaru 40 da haihuwa bai kai ba, yana haskakawa a matsayin ɗaya daga cikin matasan da s**a rungumi tsarin jagoranci cikin kwarjini da ladabi da kuma ƙware wa—ta yadda tuni waɗansu har sun fara kwatanta hasken aikinsa da tauraron Sirius da ke sararin samaniya. A matsayinsa na kakakin hukumar, yana wakiltar Hukumar Kwastam da tsantsar sanin makamar aiki, ta hanyar gudanar da ayyukansa cikin basira da kuma yin amfani da dabarun Public Relations na zamani don inganta martabar hukumar da kuma gina kyakkyawar alaka da al’umma.
A ƙarƙashin jagorancinsa, Sashen Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kwastam ya lashe kyaututtuka irinsu WCO Meritorious Award na shekarar 2024 da kuma Kyautar Mafi Ƙwazo a Fannin Yada Labarai daga NIPR a shekarar 2025. Haka zalika, a shekarar 2023, wani kamfanin dillacin labarai na Image Merchant Limited ya karrama shi da Kyautar Kakakin Hukuma Mafi Cancanta.
Duk da cewa Maiwada ya shahara a matakin ƙasa, da dama daga cikin jama’a ba su san cewa ɗan Jihar Katsina ne ba, wanda bugu da ƙari, an haife shi ne ma a Karamar Hukumar Katsina. A gaskiya, yana da ginshiƙan zuri’a masu tarihi da tasiri a ilimi da shugabanci a Arewacin Najeriya.
A bangaren mahaifinsa kuma, AC Maiwada ya fito ne daga gidan ilimi mai daraja—domin bayan kakansa, marigayi Alhaji Abubakar Maiwada—ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai a fannin Ilimi na Musamman, wato Special Education, tun daga shekarun 1960s har zuwa 1990s—hatta mahaifinsa, Alhaji Aliyu Maiwada, shi ma farfesa ne da ya karantar a Jami'ar Bayero—kafin rasuwarsa a shekarar 2020. Haka nan, tarihi ya nuna yadda kakan na sa ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa makarantu kamar Tudun Maliki Special School a Jihar Kano, wanda har ya zuwa yanzu ba a daina alfahari da shi ba. Wannan bajimin malami, shi ya haifi Farfesa Danjuma Maiwada, wanda ya kasance Farfesa na farko daga Jihar Katsina—wanda har yanzu shi ma ake alfahari da irinsa a Arewacin Najeriya.
A bangaren mahaifiya kuwa, an haife shi cikin zuriyar sarauta da ilimi. Kakan mahaifiyarsa, Muhammad Gidado, shi ne ɗan fari ga Sarkin Katsina, Sarki Dikko. Wannan zuri’a itace ta haifi Muhammad Salisu wanda ake yiwa al—kunya da Nalado, kuma shi ne kakansa na uwa, mutum mai tarin ilimi da tarihi a masarautar Katsina.
Abdullahi Aliyu Maiwada ya fara karatunsa ne na farko tun yana da ƙuruciya a cikin jami'ar Bayero ta Kano, wato Staff Primary School Kano (1992–1997), ya ci gaba da sakandire a Government Science Secondary School Dutsin-Ma dake Jihar Katsina. Bayan nan kuma ya karanci ilimin taswirar ƙasa, wato Geography Education a matsayin digiri na farko a Bayero University Kano, daga baya kuma yayi digirin—digirgir a fannin kula da muhalli, wato Environmental Management a shekarar 2011.
AC Abdullahi Maiwada ya sake komawa makaranta inda ya samu wata digirin a fannin Mass Communication da Media Arts daga Crescent University Abeokuta daga bisani ma ya zarce har zuwa karatun PhD a jami'ar tarayya dake Abuja—wato University of Abuja.
Tun bayan shiga Hukumar Kwastam da yayi a shekarar 2011, AC Maiwada ya rike manyan mukamai daban-daban. Ya fara aiki a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a a Hedikwatar Shiyyar B ta Kaduna (2013–2017), daga nan zuwa Jihar Ogun (2017–2020), kafin a dawo da shi Hedikwata a Abuja a matsayin wakilin Hukumar Kwastam a tashar NBCN. Daga nan, aka ɗaga shi zuwa Mataimakin Kakakin Hukumar na Ƙasa daga shekarar 2022 zuwa 2023. Sa'annan an naɗa shi cikakken Kakakin Hukumar (April 2023).
Yana da shaidar zama mamba a ƙungiyoyin ƙwararru da dama ciki har da Nigerian Institute of Public Relations (NIPR), African Public Relations Association (APRA), Association of Communication Scholars and Professionals of Nigeria (ACSPN) da sauransu.
AC Abdullahi Maiwada mutum ne da ke da kwazo da hangen nesa da kuma kaifin tunani wajen ganin Hukumar Kwastam ta kasance abar misali a fannoni da dama, musamman a bangaren sadarwa da wayar da kai. Yana martaba ilimi; yana aiki da kwarewa da kuma gaskiya; yana kuma kare mutuncin aikinsa da zuri'arsa da kuma jiharsa.
Wannan matsahin Bakatsinen, wanda ya fito daga tsatson ilimi a bangarori da dama, ya cancanci yabo da goyon baya daga dukkan Arewacin Najeriya—ba ma jihar Katsina ba kawai. A yau, idan ana maganar sabbin jagorori da za su shugabanci sabuwar Najeriya, tabbas Maiwada yana daga cikin fitattun matasa da s**a cancanci a amince masu.