Fact News Hausa

Fact News Hausa A wannan shafin za mu rika saka muku hotuna da bidiyo da za ku iya tafka muhawara kan su.
(3)

12/10/2025

Afuwar da Shugaba Tinubu ya yi wa Maryam Sanda da Faruk Lawan ta haifar da cece-kuce.

Idan za ku tuna an yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa a 2020 bayan zarginta da kashe mijinta Bilyaminu.

11/10/2025

Jirgin da ke dauke da tawagar Super Eagles na Najeriya ya yi saukar gaggawa a Angola.

Jirgin na kan hanyarsa ne zuwa Najeriya, inda ‘yan wasan za su buga wasa da Benin a Uyo.

11/10/2025

Yadda a ka yi Sarkin Makka ya gayyace ni aikin Hajji- N Shuraim

A wannan makon shirin ‘zo mu zauna’ ya tattauna da ‘Chilling Sheikh’ wato N Shuraim, matashin da ya samu daukaka ta fuskar addini.

Ya fada mana sirrin daukakarsa, da yadda a ka yi Sarkin Makka ya gayyace shi aikin Hajji da kuma alakarsa da M***i Menk.

10/10/2025

Ya girman matsalar damuwa ta ke a Najeriya?

Mun hada muku wannan rahoto albarkacin ranar kiyaye lafiyar kwakwalwa ta duniya.

10/10/2025

A Takaitattun labaranmu na yau za ku ji…

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta rufe matatun man fetur da ke aiki ba bisa ka’ida ba

An fuskanci tashin hankali bayan fashewar wasu abubuwa a Afghanistan

Manchester United na shirin gabatar da tayin fam miliyan 78 kan ɗan wasan Juventus, Kenan Yildiz

09/10/2025

A Takaitattun Labaranmu na Yau Za Ku Ji…

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ƙaryata rahoton Amurka kan kiristoci

Aƙalla mutum dubu ɗaya ne s**a fito zanga-zanga a Madagascar domin nuna adawa da gwamnati.

Kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes, ya ce ba shi da niyyar barin ƙungiyar a watan Janairu.

09/10/2025

Wa ne ne Joash Amupitan, sabon shugaban hukumar zabe ta Najeriya (INEC)?

08/10/2025

Ficewar Kabiru Marafa daga APC na ci gaba da janyo cece-kuce a Zamfara

08/10/2025

A Takaitattun labaranmu na yau zaku ji…

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisa don ciyo bashin sama da dala biliyan biyu

Ƙungiyoyin manyan makarantu a Najeriya za su fara yajin aikin gargadi

Super Eagles sun fara atísaye don buga wasan neman gurbin kofin duniya da Lesotho

08/10/2025

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Kano, ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan neman soke hukuncin kisa da aka yanke wa Abdulmalik Tanko da Hashim Isiyaku, kan zargin kashe Hanifa Abubakar, wadda ta ke a unguwar Dakata a jihar Kano.

07/10/2025

A Takaitattun labaranmu na yau zaku ji…

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci NAHCON ta rage kuɗin aikin Hajji

Venezuela ta lalata shirin kai hari ofishin jekadancin Amurka da ke Caracas

Atlético Madrid ta nada sabon daraktan wasanni

06/10/2025

‘Babu soyayya tsakanina da Maishadda’- Firdausi Yahaya

A wannan makon ‘Jidda’ ta fada wa mabiya shafinta gaskiyar me ke tsakaninta da Abubakar Bashir Maishadda, da kuma wani babban burinta da ke shirin cika nan gaba kadan.

Address

Wuse Zone 5
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fact News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fact News Hausa:

Share