Rariya 24/7

Rariya 24/7 enlighten Others

Yadda Jiga-jigan Ƴan siyasa A Katsina S**a Dunƙule Don Kifar Da Gwamnatin Dikko Radda A 2027 - Premium Times A siyasar N...
27/01/2026

Yadda Jiga-jigan Ƴan siyasa A Katsina S**a Dunƙule Don Kifar Da Gwamnatin Dikko Radda A 2027 - Premium Times

A siyasar Najeriya, sauyin sheƙa ana kallonta ne a matsayin neman mafita ko matsuguni ga ‘yan gudun hijirar siyasa da ke neman su kai labari. Wasu ba sa taɓuka komai. Sai dai wasu kan haifar da tasirin da ka iya kawo sauyin wajen samun mulki.

Sauyin sheƙar da Almustapha Saulawa, tsohon daraktan tsare-tsaren ayyukan ga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Masari, a ranar Talata daga jam’iyyar APC zuwa ADC misali ne na irin wannan sauyin sheƙa.

Ficewar Wasa Protocol ya tabbatar da wani lissafin da aka shafe watanni ana yin sa. Shigarsa ADC tare da tsohon tsohon sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, da wasu tsofaffin sanatoci biyu, Sadiq Yar'adua da Ahmad Babba Kaita, ya tabbatar da kafuwar wata haɗaka mai ƙarfi a jam’iyyance.

Jam’iyyar ADC a Katsina tana ƙara ƙarfi ta hanyar shigar wasu Kamar Lawal Daura da wasu Jiga-jigai wanda su ne s**a kafa tafiyar da suke ƙalubalanta a yanzu.

Da yawan wasu mutānen na ganin cewa Dikko Radda zai fuskanci kalubale a zaben 2027 duk da irin ayyukan raya kasa da ya aiwatar a jihar fadin jihar Katsina.

Saboda babu tabbas kan cewa dogaro da irin ayyukan raya ƙasa zai tabbatar da nasarar a siyasance.

26/01/2026

Kano Governor Yusuf Formally Joins APC, Welcomed By Ex-Chairman Ganduje, Others

Full story in comments section 👇🏽

26/01/2026

No Executive Order Can Stop Sit-At-Home In South-East Except Nnamdi Kanu's Release — Lawyer Ejimakor Cautions Anambra Gov Soludo

Full story in the comments section

26/01/2026

Laminu Rabiu ya yi murabus daga shugabancin hukumar alhazai na jihar Kano

Alhaji Laminu Rabiu ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban hukumar jin dadin alhazai na jihar Kano, yana mai danganta matakin da ya ɗauka da wasu sabbin sauye-sauyen siyasa da s**a faru.

A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu ya bayyana cewa shawarar ta biyo bayan tantance matsayinsa a halin da ake ciki na tafiyar siyasa.

Ya jaddada cewa har yanzu yana nan daram kan biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya da jagoranta Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, inda murabus ɗin ke nuna ƙoƙarinsa na sake daidaita matsayinsa da alkiblar jam’iyyar NNPP.

Duk da murabus ɗin, ya miƙa godiya ga Gwamnan Jihar Kano bisa damar da aka ba shi na yin hidima, tare da bayyana gamsuwarsa kan irin cigaban da aka samu wajen kula da jin daɗin alhazan jihar a lokacin da yake kan muƙamin.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin murabus ɗin a matsayin wani muhimmin sauyi da ka iya yin tasiri ga harkokin siyasa da tafiyar mulki a Jihar Kano.

26/01/2026

KARIN BAYANI AKAN KALAMAN...Hon. Danlami Kurfi Game da Matsalar Tsaro.

Zuwa Ga Al'ummar katsina Baki Daya...

Sababbin kalaman da aka danganta ga Hon. Danlami Muhammad Kurfi yayi sune da kyakkyawar niyya da zuciya ɗaya tilo dan kare al’ummar Jihar Katsina baki daya daga barazanar ‘yan bindiga da rashin tsaro. Kalaman nasa sun fito ne dan tausayi, da adalci, da ƙudurin ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan da abin yake damu. domin kauce wa duk wani ruɗani.

Mutanen da Gwamnatin Jihar Katsina ke shirin sakinsu ba ‘yan bindiga ba ne kuma ba masu laifi bane. mutane ne marasa laifi kuma waɗanda halin da s**a tsinci kansu a ciki ya jefa su cikin matsala, ciki har da ‘yan uwan ‘yan bindiga da wasu da aka k**a a yayin ayyukan tsaro ba tare da wata hujja ta kai tsaye da ke nuna sun aikata laifi ba. Sakin nasu mataki ne na samar da zaman lafiya, ba goyon bayan aikata laifi ba, kuma ana sa ran hakan zai taimaka matuƙa wajen kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Katsina.

Hon. Danlami Kurfi ya sake nuna cewa shi shugaba ne mai son al’ummarsa kuma mai fifita rayuwa da walwalar jama’a ne. Haka kuma, shi babban mai goyon bayan Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ne kuma yana mara masa baya dari bisa dari wajen aiwatar da manufofinsa na tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da ci gaban jihar katsina.

Maimakon s**ar kalamansa ko mayar da su siyasa don amfanin kai, ya dace jama’a su godewa Hon. Danlami Kurfi tare da yaba masa, domin tsayuwarsa kan gaskiya, haɗin kai, da zaman lafiya. Matsayinsa ya nuna gaskiya, jarumtaka, da biyayya ga jama’a da kuma gwamnatin Jihar Katsina.

Abin takaici ne cewa wasu daga cikin masu adawa da gwamnati da kuma wannan shiri sune waɗanda basa fatan a kawo ƙarshen ‘yan bindiga, da matsalar tsaro a jahar katsina domin suna amfana da matsala ta insecurity, kuma basa son ganin Gwamnatin Jihar Katsina ta yi nasara.

Saboda haka, ana kira ga al’ummar Jihar Katsina da suyi watsi da labaran ƙarya, su kasance masu haɗin kai, tare da ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin gwamnati domin samar da Jihar Katsina mai aminci, da zaman lafiya, da kuma ci gaba.

Wannan sako ne daga Kungiyar - Danlami Kurfi Support Team.

Address

Jabi
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rariya 24/7 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category