
30/07/2025
An Saki Mukhtar Bayan Shafe Shekara Daya a Gidan Yari Saboda Zargin da Ba Shi da Tushe
Abuja, Najeriya — 30 Yuli, 2025
An saki wani matashi mai suna Mukhtar daga gidan yari bayan kotu ta yanke hukunci da cewa babu ci gaba da gurfanar da shi bisa doka, sannan ta soke karar da ake masa tun shekarar 2023.
Mukhtar ya shiga hannun hukuma ne bayan wani abokinsa ya zarge shi da hannu a cikin wani damfara da ya shafi lambar c**a. A cewar lauyoyinsa, Mukhtar ne ya fara siyan wata lamba daga wani mutum da ya yi alkawarin za ta kawo masa nasara har Naira miliyan ɗaya bayan ya biya N50,000. Bayan hakan bai yi nasara ba, sai ya bada bayanin ga wani abokinsa.
Abokin ya nemi wanda ya bayar da lambar kai tsaye, inda ya biya kuɗi da nufin samun lamba da za ta kawo masa Naira miliyan 50. Sai dai dukansu aka yaudara, mutumin ya tsere da kuɗinsu. Amma abin mamaki, Mukhtar ne aka k**a aka tsare bisa zargin hannu a damfara.
Tun daga lokacin, ya cigaba da zama a gidan yari, yayin da shari’ar ke ci gaba da jan dogon lokaci sak**akon kin halartar kotu da bangaren masu ƙara ke yi. Lauyoyinsa daga Abuja sun nemi kotu ta soke karar saboda rashin kulawa da gurfanarwa daga masu ƙara, kuma kotu ta amince.
Lauyoyin sun bayyana cewa lamarin ya nuna irin sauƙin da ake damƙe marasa laifi a tsarin shari’ar Najeriya. Sun kuma yi kira da a sake duba yadda ake gudanar da bincike da tuhuma kafin k**a mutum.
Mukhtar ya samu 'yanci, amma ƙalubalen da ya fuskanta ya bar darasi mai nauyi ga tsarin shari’a.