26/02/2024
KO KUN SAN WANNAN MASALLACIN SHINE NA UKU MAFI GIRMA A DUNIYA
An Kaddamar da katafaren masallacin mai suna 'The Great Mosque of Algiers' wanda shine mafi girma a Afirka dake a birnin Algiers sannan kuma na uku mafi girma a duniya.
Shugaban Kasar Algeriya, Abdulmadjid Tebboune ne jagoranci kaddamar da masallacin.
Bayan masallatai masu tsarki na Makkah da Madina sai wannan Masallacin, wanda girmansa ya kai kadada saba'in sannan mutum 120,000 ne za su iya yin ibada cikin sa lokaci guda.
Hakazalika Masallacin na da hasumiya mafi tsawo da ake amfani da ita wajen kiran sallah.
An gina masallacin cikin shekara bakwai inda kuma aka kashe sama da dala miliyan 800,000 wajen gina shi.
Ana sa ran za a rika gudanar da salloli a lokacin watan Ramadan da ake shirin farawa nan da mako biyu masu zuwa.
Masallacin wani aiki ne na tsohon shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ya sauka daga kan mulki a 2019 bayan yunkurinsa na neman wa'adi na biyar ya janyo gagarumar zanga-zanga.