06/04/2024
DAN AREWA DA WAWAN TUNANI (1)
Ya ishi mutum Jarrabawa Allah yayi shi a Nigeria kuma Arewacin Nigeria, domin kuwa In Allah ya Azurta mutum da Fahimtar abubuwan da suke faruwa a kewaye dashi gwargwadon hali, to kullum zai dinga kwana yana tashi cikin damuwa da halin da al'umma take ciki.
To saide ita kuma Al'ummar mafi yawanta basa lura , kuma basa gane hakikar halin da suke ciki, kuma suna gaba da duk mai kokarin Nuna musu wannan halin da suke ciki domin a fara kokarin samo hanyoyin maganin matsalar.
To ya zakayi da wanda Baima yadda yana cikin matsala ba b***e ya fara tunanin hanyar Da zaibi domin Maganin ta ?
Idan ka duba a kewaye dakai sai kaga wani mutum wanda Malaman sa s**a hana masa 'Yancin yin tambaya, sannan s**a hana masa 'Yancin yin bincike, Saide abin da s**a fada masa kadai shin ma'auninsa, idan kace dashi, Ya kamata ya dinga Tambaya sannan ya dinga bincike domin nemawa kansa amsosin wasu daga matsalolin da s**a dameshi , sai yace dakai , ai tunda akace dashi karya yayi tambaya kuma kar yayi bincike, to Ya Yarda, kuma matsayar da kenan , To irin wannan mutum Ya zakayi dashi ?
A wanan Al'ummar tamu ce zaka waiga kusa dakai sai kaga wanda wanda Aka baiwa wani hakkinsa ta hannun wani , shi wanda Aka baiwa hakkin nasa ya bashi ya cinye masa hakkin nasa, Saika bashi shawara kace, kaga tunda an baiwa wane Hakkin ka kuma ya cinye kana iya bin kadin hakkin ka dalilin da yasa ma akayi kotu da jami'an tsaro kenan , Sai Shi kuma yace dakai , ai Ba rabo bane domin Allah ne bai nufi kudin su iso gareni ba, idan kuma kace dashi Ai Allah ya riga ya bashi wanine ya cinye masa, Sai yace dakai Baka da Tauhidi, saboda kaki yadda da kaddara.
to ya zakayi da irin wanan mutum wanda bisan Dalilin da Yasa Allah zai yi Hisabi shine saboda wasu bayi suna cinye hakkin wasu bayin. ?
A wannan yanayin na kunci da damuwa da wasu mutane s**a jefa al'umma a ciki da gangan idan kayiwa mutane da dama bayanin haka basa ganewa sai s**e ai Allah yaso ya gansu cikin wannan Kangin Bauta kunci da damuwa.
Idan kace dasu ai Tunda Allah ya ajiye Arziki na Zinariya, Azurfa, kasar noma , man Fetur, Iskar gas, Kogonni, Hasken rana da sauransu, Ai ya baku arziki, sai yace dakai ai A'a ai hakkin amfani da wannan Azikin masu mulki ne kadai suke dashi , idan ka tambaye shi to Meyasa masu Mulkin basa amfani da arzikin wajen inganta rayuwar al'ummar kasar?
sai yace dakai wai Allah ne bi nufiasu mulkin da suyi Adalci ba, Ya yadda ya jingina Mummuna ga Mahalicci akan ya jingina ga Mai Mulkin da yake zaluntar sa, shin ya zakayi da irin wadannan mutanen ?
A wannan Kasa tamune Azzaluman masu mulki s**a gano Amfani da malamai wajen Kamfen na siyasa shi yafi komai sauki, Ga Araha ga Biyan buƙata, Sannan Ga kariya ta musamman a duniya, su tafka sata da gangan mai gurgunta tattalin arziki, Daga sun ɗan sanya Malamai na Fada kadan , shikenan, sai a jinginawa Allah kuncin da Satar Azzalumin mai mulki ta Kawa talakawa, shinen Sai ace da talaka ai Tauhidene jure wannan kuncin rayuwa kuma akwai lada mai girma.
haka nan talaka zai yarda kuma yayi biyayya da nufin samun lada, bayan Malam ya dade da karbar nasa ladan daga cikin hakkin talakawa da aka sace.
shin ya zakayi ka Fahimtar da irin wadannan mutanen cewa Ba Allah ya dora masu Kunci da wahalar rayuwa ba, hakan ya faru ne saboda wasu sun sace Arzikin da ya kamata ayi amfani dashi wajen saukaka wa rayuwarsu?
Jarrabawace ta Kasancewa a cikin wannan Al'umma wacce aka haÉ—u masu mulki da Malaman Fada aka daure mata Kwakwalwar ta , aka hana ta tunani mai kyau akan mokomarta , aka hanata duk wani yunkuri ko motsin da zai kai ga 'Yantar da kanta.
Ana cutar da ita ta hanayar amfani da imanin ta addininta da riko da Malaman ta shugabanninta.
Shin Zang-Zanga tana da Amfani kuwa wajen kwatar kai daga Kangin Bauta ?
Shin Zanga Zanga a Nigeria akan wani abu da yake faruwa a Duniya Tana da wani Tasiri a wancan muhallin ?
Shin Idan Aka samu Nasarar Kwace wa Al'umma'Yancin yin Zanga Zanga mai zai iya biyu baya ?
Mu hadu a Rubutu na Gaba.
~Ibn Abubakar Alhausawy