19/08/2025
TA AD'DANCI MAFI MUNI A KARAMAR HUKUMAR MALUMFASHI, KATSINA STATE, INDA YAN TA'ADDA S**A BUDEWA MASALLATA WUTA A DAIDAI LOKACIN DA SUKE GUDANAR DA SALLAR ASUBA..
Da Asubahin Ɗazu Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wuta Ga Masallata Sun Hallaka Mutum 27 A Gidan Mantau Dake Ƙaramar Hukumar Malumfashi.
Ta'addancin da waɗan nan ƴan bindiga s**ai da asubahin dazu ga wasu masallata a ƙauyen gidan Mantau dake yankin Karfi, Ward cikin ƙaramar hukumar Malumfashi, shine ta'addan ci mafi muni a wannan lokaci kuma a wannan yanki na ƙaramar hukumar Malumfashi.
Kawo yanzu ba'a kaiga gama tantance rahotan adadin iya barnar da ƴan bindigar s**ayi ba amman dai izuwa yanzu an samu rahotan shigar ƴan ta addan dazu a ƙauyen na Gidan Mantau, sun buɗewa masallata wuta da anan take mutum 16 Allah Yayi musu cikawa.
Kana sun kashe wasu mutanan a cikin gari sun kuma ƙona wasu gidajen Al'Ummah, sun kuma raunata mutane da dama da aciki yanzu ake ƙara bada rahotan mutuwar wasu da gabadaya yanzu mutun 27 ne s**a rasa ransu a sak**akon wannan mummunan hari da ƴan ta'addan s**a kai a yau Talata 19-Aug 2025
Ƴan ta'addan sun kuma kwashi mutane mata da a kalla zasu kai 60 a yanda mutanen garin s**a ce.
Mako biyu a baya da s**a gabata mutanen yankin sunyi nasarar kashe mutum uku a cikin ƴan ta'addan kafin yanzu suyi wannan shigar da ake ganin k**ar dai dama ɗaukar fansa ƴan ta'addan s**a zo.
Tun dazu da Safe har yanzu haka dai halin da ake ciki mutanan yankin da wasu makusanta sun fito sun tare hanyar marabar ƙankara har zuwa hanyar kan kwanar ABU inda nan ne hanyar shigowa tsakiyar cikin garin Malumfashi, duk sun rufe hanyar babu wujen wucewa ta ababen hawa.
Ana ganin mutanan sunyi haka ne dan nuna tabbacin damuwar su ga gomnati da al,ummar duniya akan halin da suke ciki na wannan ta'addanci da yake faruwa kullum a yankin su kuma gashi anƙi a ɗauki matakin kawo ƙarshen lamarin duk da gashi Ana ta kashe su a kullum dare da rana.
haka idan ka shiga tsakiyar cikin garin Malumfashi nan kuma kusan duk inda ka zaga zaka ga ƴan gudun hijira ne sun kwaso kayan su sun tafi batare da sunsan ko ina s**a nufa ba, wasu makarantun firamari suma haka suna Chan a cike da mutane ƴan gudun hijra.
Idan ka ziyarci bangaren assibitoci Nan ma general Hospital assibitin kwandala dake cikin garin Malunfashi nacen cike k**ar kwata da jinin masu buƙatar agajin gaugawa da ƴan ta addan s**a harba a yau ko jiya ko kuma dai wani lokaci a cikin ƴan kwanakin nan.
ALLAH YA KAWO MANA SAUQI BAKI DAYA.
Source : Daga| Kamala Bala Kamalancy
19| Aug| 2025