03/09/2026
TIRKASHI: Kai da ka kasa rage farashin ruwan FARO ne kake alkawarin rage farashin man fetur? — Dr. Sani Ahmad Zangina ya caccaki Atiku
Dr. Sani Ahmad Zangina ya ƙalubalanci Atiku Abubakar kan alkawarin rage farashin man fetur, yana mai cewa ya kamata ya fara da rage farashin ruwan FARO da kamfaninsa ke samarwa.
Dr. Sani Ahmad Zangina ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan alkawuran da yake yi wa ’yan Najeriya na rage farashin man fetur da kuma batun tallafin mai gabanin zaɓen 2027.
Zangina ya ce idan har Atiku na son tallafa wa talakawa da rage musu radadin tsadar rayuwa, ya kamata ya fara daga kamfaninsa ta hanyar rage farashin ruwan sha na FARO da sauran kayayyakin da kamfanin ke samarwa.
A cewar Zangina, ruwan FARO da talakawa ke amfani da shi a kullum ya yi tsada, duk da cewa kamfanin na cikin harkokin kasuwancin Atiku.
Ya ce abin mamaki ne mutum ya kasa rage farashin ruwan sha da talakawa ke saya a kullum, amma a lokaci guda yana yi wa ’yan Najeriya alkawarin rage farashin man fetur daga N145 zuwa N90.
“Kai da ka kasa rage farashin ruwan FARO ne kake alkawarin rage farashin man fetur ga sama da ’yan Najeriya miliyan 200?” in ji Zangina.
Zangina ya kuma ce ya kamata ’yan Najeriya su tuna da irin alkawuran da ’yan siyasa ke yi a lokacin neman zaɓe, yana mai kira ga Atiku da ya daina, a cewarsa, yaudarar ’yan Najeriya da alkawuran da ba za su cika ba domin samun nasara a zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa “alheri yana farawa ne daga gida”, yana mai cewa idan ba a iya sauƙaƙa wa talakawa farashin abin da ake samarwa a kamfani ba, to akwai tambaya kan yadda za a iya aiwatar da irin wannan tsari a faɗin ƙasa.