14/10/2025
NANA AISHA TANA KOYAMA MAZA WANKAN JANABA AIKACE 🙆😥
Shin kai ma ka bada aron hankalinka ? Idan kana cikin masu bada aron hankalinsu, Ina son nima ka bani aron hankalin naka na minti biyar, sannan ka karɓo abinka, sannan kayi nazarin wannan karatun da zan biya maka kyauta, ba tareda karɓar ko Sisin kwaɓo daga gareka ba, na albarka makaranta.
Hadisi ne ɗaya zan kawo muku tareda fitar da mushkilolin da yake ɗauke dasu, sannan mu bijirar da hadisin zuwaga hannun Malamai Magabata mu gani ko sunyi wani bayani na Ilmi da hankali da zai warware waɗannan ishkalatun dake cikinsa.
GA LAFAZIN HADISIN 👇
صحيح البخاري - كتاب الغسل - باب الغسل بالصاع ونحوه.
248 - حدثنا : عبد الله بن محمد ، قال : حدثني : عبد الصمد ، قال : حدثني : شعبة ، قال : حدثني : أبو بكر بن حفص قال : سمعت أبا سلمة يقول : دخلت أنا وأخو عائشة على عائشة فسألها أخوها عن غسل النبي (ص) ، فدعت باناء نحوا من صاع فاغتسلت وأفاضت على رأسها وبيننا وبينها حجاب ، قال أبو عبد الله ، قال : يزيد بن هارون وبهز والجدي ، عن شعبة قدر صاع.
Daga Abu Salamata ya ce : Na shiga ni da ɗan uwan Aisha inda aisha, sai ɗan uwanta ya tambaye ta akan siffar wankan Annabi s.a.w ? Sai nana Aisha tace : A kawo mata makai/ abin zuba ruwa kwatankwacin yawan sa'i, sai tayi wanka ta zubama kanta ruwa, alhali tsakanin mu da ita akwai shamaki.
Ba Bukhari kaɗai ya ruwaici wannan hadisin ba , Muslim, Nasa'iy, Ahmad ɗan Hanbali da waninsu duka sun ruwaici wannan hadisin.
ABIN LURA CIKIN WANNAN HADISIN
Dan uwan nana Aisha da s**a sha nono tare, shine yazo tareda wani suna tambayar Aisha ya Annabi s.a.w yake wankan janaba. Sai nana Aisha tasa aka kawo ruwa ta tashi ta nuna musu yadda ake wankan janaba aikace suna kallonta.
Sanin kowane su tambayarta s**ayi, watoh bayani suke nema bayani na fatar baki, ba a aikace s**ace a nuna musu yadda ake wanka ba, amma sai akace ta koya musu ma'ana ta gwada musu yadda ake wankan aikace.
Shin annabi saw ya taba nunama wani yadda ake wankan janaba aikace ?
Shin ana wanka sanye da tufafi ko sai an tube ?
Ance tasa kariya tsakaninta dasu. In ansa kariyar ya a kayi s**aga yadda tayi wankan aikace bayan tasa shamaki basu gani ?
In tasa kariya toh miye fa'idar yin wankan aikace, alhali waɗanda ake koyama basu ganin mai koya musu bale har suga abin da yake koyamusun ?
Shin akwai mutunci yanzu babarka, ko yar uwarka tazo tana wankan gaban idonka ?
SHARHIN WANNAN HADISIN
Wawaye da jahilai in muka ciro IRE-IREN wadannan hadissan, suna kokarin cewa an munana fahimta, bamu gane ba, ba haka magabata s**a fahimta ba. Saboda haka zamu leka masharhanta mujiya shin sunyi wani gamsarshen bayani akan wannan kwamacalar ko kuwa.
Ibnu hajar cikin fathul bary ya kawo sharhinsa yace :
قال القاضي عياض - رحمه الله تعالى – لما قال : "ظاهر الحديث أنهما رأيا عملها في رأسها وأعالي جسدها مما يحل لذي المحرم النظر إليه من ذات المحرم.
Alkali iyadd yace
Zahirin hadisin nan, yana nuna cewa sunga aikin nana Aisha, cikin wanke kanta da saman jikinta, daga inda ya halatta muharrami ya gani na jikin muharramarsa.
ولولا أنهما شاهدا ذلك ورأياه لم يكن لاستدعائها الماء وطهارتها بحضرتهما معنى، إذ لو فعلت ذلك كله في ستر عنهما لكان عبثا ورجع الحال إلى وصفها له، وإنما فعلت الستر ليستتر أسافل البدن , وما لا يحل للمحرم نظره والله أعلم"
Ba don da sunga hakan (wankanta) da idanunsa aikace ba, da babu wata ma'ana cikin kawo mata ruwa da yin wankan a gabasun ba. saboda da tayi wankan boye bayan idanunsa, daya kasance wasa ce kawai ta keyi da kanta, kuma kanta ne kawai ta siffantama wankan ba su ba. Sai dai cewa duk da haka tasa kariya domin ta rufe kasan jikinta, da inda baya halatta muharrami ya kalla.
Shima malam Quurdubiy haka ya fada yace
فقال: "ظاهر هذا الحديث أنهما أدركا عملها في رأسها وأعلى جسدها ، مما يحل لذي المحرم أن يطلع عليهِ من ذوات محارمه ،.
Zahirin wannan hadisin yana nuna cewa sunga wankanta, cikin wanke kai da saman jikinta, daga cikin abinda ya halatta muharrami ya tsinkaya na jikin muharramarsa.
Dan Uwa domin sanin iyakar inda ya halatta muharrami ya kalla na jikin muharramarsa, ka koma littafan fiqhu, anan ne zaka san waɗannan Bayin Allah n masu sharhi ƙara lalata lamarin nan kawai s**ayi, kwaɓa ce kawai s**a ƙaramar ruwa.
Abinda Malaman Fiqhu suke cewa akan abin da ya halatta mutum ya gani daga jikin yar uwarsa mace ko mamarsa ko wata muharramarsa, shine " Daga cibiyar mace har zuwa mammanta ya halatta muharraminta ya gani" ma'ana dai su waɗannaj mutum ne biyu da ɗan uwan Nana A'isha wanda s**a sha Nono tare da ita da abokinsa ɗayan, iyakar abinda s**a ganin na jikinta shine daga cibiyar ta har zuwa qirjinta y😥
Jama'ar Annabi saw Abin baqin cikin shine Maluman nan duka sun kauda kai daga cewa shi fa wannan ɗan uwanta da s**a sha nono ɗaya da ita, ba shi kaɗai yake ba, yana tare da wani mutum na daban, kuma shima wannan mutanen tare da shi akazo yin tambayar ya ake wankan nan, tare da muharraminta yaga abinda su suke qoqarin cewa shine ya halatta muharramin ya gani daga muharramarsa 😥 ma'ana daga Cibiyarta zuwa Ƙirjinta.
Da irin wannan shirmen suke sharhantar ire-iren waɗannan hadissan da babu komi cikinsu sai buɗe hanyar raina Ma'aikin Allah Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam da Iyalinsa.
Wannan fa su Ibnu Hajar, Alqadi Iyad da Qurɗabiy kenan, da irin wannan kwamacalar aka sharhanci wannan hadisin, bale waɗannaj shirmammun malaman media na yanzu ! Yanzu wannan sharhi ne ko dai ƙara sharri akan sharri ne ?
Duk wannan abin fa kawai isnadi ya inganta, sai su kauda kai da qa'idar da su ne s**a rubuta a littafan su cewa ko isnadi ya inganta ya zamana maganar dake ƙarshen sarqar ta zamana mai kyau mai ma'ana !