20/08/2025
Duk wanda ya saurari tattaunawar DCL da ɗan bindiga Kachallah Dan Sadiya zai ƙara fahimtar wannan hanyar ta sulhu domin samar da zaman lafiya ita ce mafita.
A cikin tattaunawar ya yi wata magana wacce ya kamata al'umma su yi nazari su lura, ya bayyana cewa su da su ke wannan ta'addancin a haka akwai ɓurɓushin ilimi a tare da su, amma ragowar masu tasowa ba su da ilimi ko kaɗan, kenan abin a gaba zai ƙara ƙazancewa ne.
A cikin tattaunawar ya bayyana dalilan su na ɗaukar makami, duk wanda ya saurari dalilan na su, zai fahimci tattaunawa da su domin samar da sulhu shi ne zai magance wannan matsalar.
Wannan ya na ƙara fito da gaskiyar tasirin da sulhu zai yi wanda bindiga ba za ta yi ba, domin ana yaƙar su da bindiga har yanzu, amma ba su dena ba, amma a yankunan da aka samu nasarar sulhu an dena wannan ta'addancin, kenan sulhu shi ne mafitar kawo ƙarshen wannan ta'addanci.
Duk wanda ya san yadda Birnin Gwari ta ke a shekarun baya zai tabbatar da amfani sulhun nan, domin a irin yanayin da yankin ya shiga da kuma yadda aka samu zaman lafiya a yanzu ya na ƙara tabbatar da yadda sulhun ya kasance alheri.
Wannan sulhun da kwamitin Sheikh Musa Asadussunnah ya ke jagoranta muna fatan Allah ya ba su nasara, Allah ya magance mana matsalolin tsaron da ke addabar Najeriya.
Allah ya yi mana maganin ƴan ta'adda da ta'addanci a Najeriya.
Ibrahim Imam Ikara
20 August, 2025.