21/10/2025
Comr. Idris Adamu Halilu Ya Saya Fom ɗin Takara na Shugaban Ƙasa na NUBASS
Ɗaya daga cikin fitattun matasan Bauchi State a fagen shugabancin ɗalibai, Comrade Idris Adamu Halilu, ɗalibi mai karatun Political Science a Sa'adu zungur university (SAZU), ya sayi fom ɗin nuna sha’awa da na takara domin neman kujerar Shugaban Ƙasa na Ƙungiyar Daliban Bauchi State (NUBASS National President) a babban taron ƙasa mai zuwa.
Bayan sayen fom ɗin, Comr. Idris ya bayyana godiyarsa ga iyaye, ‘yan uwa, dalibai, da manyan jiga-jigan NUBASS da s**a ba shi goyon baya da shawarwari kafin ya yanke shawarar tsayawa takarar.
Ya bayyana cewa manufarsa ita ce inganta haɗin kai, walwala da tsaro ga dukkan ɗaliban Bauchi State, tare da ƙarfafa damarmaki na ci gaban ilimi da sana’a.
Manufarsa ta taƙaita ne a kan muhimman abubuwa uku:
1- Tallafin Karatu na Ƙasa da Ƙetare (International Scholarship) — neman haɗin gwiwa da ƙasashe da cibiyoyi domin samun damar karatu da musayar kwarewa ga ɗaliban Bauchi.
2- Magance Matsalar Barin Makaranta da Rashin Tsaro (School Dropouts and Insecurity) — aiki tare da hukumomi da al’umma wajen ganin matasan Bauchi suna kammala karatunsu cikin tsaro da kwanciyar hankali.
3- Walwalar Dalibai (Students’ Welfare) — tabbatar da biyan tallafin karatu cikin lokaci, samar da JAMB ga marasa galihu, da ƙirƙirar hanyoyin tallafi da horo ga ɗalibai.
Comr. Idris ya ce kasancewarsa ɗalibin Political Science ta koya masa mahimmancin shugabanci mai gaskiya da jagoranci na amana.
Ya jaddada cewa zai jagoranci kamfen mai tsabta, haɗin kai, da neman ci gaba wanda zai mayar da hankali ga dalibai ba siyasa ba.
“Shugabanci ba mulki ba ne — hidima ce ga jama’a,” in ji Comr. Idris Adamu Halilu.