ZAKI DAILY News HAUSA

ZAKI DAILY News HAUSA Zaki Daily News Hausa | Media And News Company | Advertising

YANZU-YANZU: An yi Jana'izar ga'ib ga ruhin marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a KanoAn gudanar da jana'izar Marigayin a Masa...
28/06/2025

YANZU-YANZU: An yi Jana'izar ga'ib ga ruhin marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a Kano

An gudanar da jana'izar Marigayin a Masallacin Umar Bin Khattab, a Dangi da ke Kano
Allah Ya Masa Rahama

Masha Allahu Ya Allah Muna Rokonka Da Katabbatar manaZAKI DAILY News HAUSA
28/06/2025

Masha Allahu Ya Allah Muna Rokonka Da Katabbatar mana
ZAKI DAILY News HAUSA

27/06/2025
Barkanmu da Yamma
14/06/2025

Barkanmu da Yamma

31/05/2025

Yaa Allah duk Musulmin da bashi da halin yin Layya Ka bashi ikon yi don RahamarKa Yaa Allah🙏

Da Dumi Duminta:Ga garurrukan da zasu shiga fari na tsawon kwana 21 zuwa sama a tsakanin June zuwa August a arewacin nig...
29/05/2025

Da Dumi Duminta:Ga garurrukan da zasu shiga fari na tsawon kwana 21 zuwa sama a tsakanin June zuwa August a arewacin nigeria. Sai a sanar da manoma dan Allah.

Wannan hasashen hukumar "NiMet" ne ta yi shi. Nima a wajen su na ɗauko. Allah ya kiyaye mu da fari. Ameen.

Yana da kyeu ƙungiyar manoma su dinga saka ido akan binciken da "NiMet" take yi na ko wani shekara, zai taimaka musu sosai. Yana daga cikin abunda nake karantarwa a karatun Meteorology.

To wannan shine, Allah yasa mu dace. Ameen Thumma Ameen. inji Tijjani Aliyu
ZAKI DAILY News HAUSA

DA DUMI DUMINTA:Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzu bashin da ake bin Nijeriya yana dab da kai wa Naira Tiriliyan ₦162.02...
28/05/2025

DA DUMI DUMINTA:Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzu bashin da ake bin Nijeriya yana dab da kai wa Naira Tiriliyan ₦162.025 da zarar Shugaba Tinubu, ya samu sahalewar Majalisun Tarayya na sake ciyo sabon bashin Tiriliyan 17 akan tsohon bashin da ƙasar ke da shi.

Hakan zai iya ƙara yawan bashin da ake bin kowane ɗan Nijeriya idan aka kasafa kuɗin ga kowane ɗan ƙasa, daga Naira 450,000 zuwa Naira 810,000. Shin menene ra'ayoyin ku..?
Domin Samun Labarai Shigo Jaridar ☆ ZAKI DAILY News HAUSA ☆

DA DUMI DUMINTA: ☆Masana Siyasa Sun Bayyana cewa ga Jerin  jihohin da ake sa ran kowanne dan takarar shugaban zai lashe ...
28/05/2025

DA DUMI DUMINTA: ☆Masana Siyasa Sun Bayyana cewa ga Jerin jihohin da ake sa ran kowanne dan takarar shugaban zai lashe zaɓe a 2027.

BOLA TINUBU:
1-Osun
2-Ekiti
3-Ondo
4-Oyo
5-Lagos
6-Ogun

ATIKU ABUBAKAR:
1-Adamawa
2-Benue
3-Delta
4-Edo
5-Akwa Ibom
6-Rivers
7-Cross Rivers
8-Bayelsa
9-Abuja
10-Gombe
11-Bauchi
12-Abia
13-Anambra
14-Enugu

RABIU KWANKWASO
1-Kano
2-Katsina
3-Kaduna
4-Jigawa
5-Naija
6-Sokoto
7-Zamfara
8-Abuja
9-Taraba
10-Borno
11-Yobe
12-Kwara
13-Kogi
14-Kebbi
15-imo
16-Ebonyi

Kuna Son duba Sahihan Labarai Shigo Gidan Jaridar ☆ ZAKI DAILY News HAUSA ☆ Yanzu Yi Following Karku Bari Komai Ya Wuceku...

Ba zan sake halartan taron jam’iyyar `PDP` ba har sai an kori Wike da Ortom ☆ Inji Sule LamidoWato ainihin Tsohon Gwamna...
28/05/2025

Ba zan sake halartan taron jam’iyyar `PDP` ba har sai an kori Wike da Ortom ☆ Inji Sule Lamido
Wato ainihin
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, a matsayin annoba da ya kamata a kore shi daga jam’iyyar PDP.

Lamido ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi da shi a Abuja a jiya Talata.

Ya bayyana cewa ko da yake har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, wacce ya taimaka wajen kafuwa ya yanke shawarar dakatar da halartar tarukan shugabanci na jam’iyyar – duk da zafin hakan – matuƙar Wike da tsohon Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, na ci gaba da zama mambobin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar.

Tsohon gwamnan ya yi mamakin yadda ake kokarin tilasta wa jam’iyyar karɓar Sanata Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren jam'iyyar na ƙasa, duk da cewa yankinsa, gwamnoni da Kwamitin Amintattu (BOT) sun ƙi amincewa da shi.

A lokacin da aka tambaye shi game da rawar da Wike ya taka wajen rufe ofishin PDP na ƙasa, Lamido ya ce: “To, me mutum zai ce? Wannan ai wani wasan kwaikwayo ne na siyasar Najeriya.
``Ga mutum wanda PDP ta girmama, ta ba shi matsayi, yanzu kuma ya dawo yana yakar jam’iyyar da ta kawo shi. A gaskiya, Wike annoba ne. Abin da yake yi ba dabi’ar Afirka bane, ballentana ta Najeriya,
ZAKI DAILY News HAUSA

Numfashi ko iskar numfashi (Oxygen) da ake sakawa mara lafiya a Asibiti duk Awa daya ana biyan Naira dubu 5,500 (daga ka...
27/05/2025

Numfashi ko iskar numfashi (Oxygen) da ake sakawa mara lafiya a Asibiti duk Awa daya ana biyan Naira dubu 5,500 (daga karfe 1 zuwa karfe 3 Naira dubu 15,000 sun tashi a aiki), idan kana da mara lafiyar da aka dora shi akan Oxygen na tsawon Awanni 24 zaka biya Naira ₦132,000 a kowace rana.

~ Hakan yana nuna duk sati (weekly) zaku biyawa majinyacin ku Naira dubu ₦924,000
Wannan yana nuna duk wata zaka biya Naira miliyan ₦3,696,000

Duk shekara Naira ₦44,352,000.

Idan shekarar ka 25 a duniya kuma ba'a taba saka maka Oxygen din Asibiti ba, ka samu kyautar Oxygen daga wajen Allah madaukakin sarki na Naira biliyan ₦1,108,800,000 a tsawon shekaru 25 da kayi a duniya.

Idan shekarar ka 30, Allah ya baka Oxygen na Naira biliyan ₦1,330,560,000.

Mai shekaru 45 ya samu kyautar Oxygen daga mahaliccin sa na Naira biliyan ₦1,995,840,000.

Mai shekaru 50 kuma yasha Oxygen na Naira biliyan ₦2,217,600,000.

Da ace za'a bar mu da biyan kudin numfashi da dan Adam ya gane shi ba kowa bane.

A cikin Suratun Nahli Allah yace
ZAKI DAILY News HAUSA

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ZAKI DAILY News HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category