17/09/2025
Abba Anwar ya kalubalanci Ganduje kan Ayyukan Harkar Ilimi a Kano ta Arewa
Tsohon babban sakataren yada labaran tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Mallam Abba Anwar ya kalubalanci Ganduje, kan rashin tabuka abun a zo a gani a bangaren ilimi, k**ar yadda mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril ke yi, a yankin Kano ta Arewa.
A cewar Abba Anwar, Sanata Barau ya zama jigon tallafawa bangaren ilimi, wanda bashi da sa'a a gaba dayan Kano ta Arewa, duba da wasu manyan ayyuka da ya gudanar, wanda s**a daga darajar ilimi a jihar Kano.
Duk da yake dai cewar shi Anwar din bai fito fili ya k**a sunan Gandujen ba, a wani rubutun sa da ya sa a shafin sa na Facebook kuma a ka buga a jaridar Daily Trust da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo.
Amma kasancewar ya kalubalanci duk wasu masu rike da muk**ai a gwamnatin tarayya, wadanda a ka zaba da kuma wadanda a ka nada, da su ka fito daga shiyyar Kano ta Arewa. Wato bangaren da Sanata Barau ya fito. Shine kuma bangaren da Gandujen shi ma ya fito.
Ayyukan da Sanata Barau a bangaren ilimi sun hada samar da Jami'ar Kimiyya da Fasaha gwamnatin tarayya a ƙaramar hukumar Kabo, tare da ɗaukar nauyin matasa su Saba'in (70), zuwa kasashen waje dan karo karatun Digiri na Biyu a bangarori daban daban.
A bangaren jam'i'o'in ciki gida, Sanata Barau ya dauki nauyin karatun dalibai Dari Uku (300) domin yin Digiri na Biyu, a manyan jam'i'o'i irin su BUK, ABU, Jami'ar Lagos, da jami'ar Ibadan da sauran su, yayin da Sanatan ya fi maida hankali kan fannonin da a ke alfahari da su yanzu a duniya.
A bangaren masu digiri na farko, Sanata Barau Jibril ya dauki nauyin karatun dalibai sama da Dubu Biyu (2,000) domin karantar bangarorin karatu daban daban a shiyyoyin jami'ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma da suke nan Kano, wadanda shi ne silar samar dasu.
Idan za a iya tunawa tun kafin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya yi iya kokarin sa wajen ganin an bude cibiyoyin karatu na National Open University of Nigeria (NOUN), a kowace karamar hukumar da take karkashin wakilcinsa. Wato a kananan hukumomi 13 dake a Kano ta Arewa.
A don haka ne Abba Anwar ke ganin cewa lallai Sanata Barau yayi zarra wajen tallafawa bangaren, inda ya kalubalanci tsohon mai gidansa Ganduje, amma a fakaice tare da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf su yi koyi da Sanata Barau wajen tallafawa bangaren ilimi.
Amma wani bincike da a ka yi an gano cewar tabbas Gandujen bai tallafi harkar ilimi a bangaren Kano ta Arewa din ba a gaba daya shekarunsa takwas a kan karagar gwamnatin Kano, k**ar yadda Barau din ke yi a wadannan lokuta.
Musamman idan a ka duba irin daukar nauyin karatun dalibai tululu dan karatu a ciki da wajen Najeriya ba. Musamman kuma idan a ka kalli irin fannonin ilimi na zamani da Sanatan ke daukar nauyi.