
29/07/2025
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Daukar Ma’aikata a Mataki na Biyu na Shirin Renewed Hope Ta Ƙarƙashin Hukumar NDE
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da mataki na biyu na daukar ma’aikata karkashin shirin Renewed Hope Employment Initiative (RHEI) ƙarƙashin Hukumar Kula da Ayyukan Yi (NDE), domin rage rashin aikin yi da kuma koyar da matasa dabarun samun sana’o’i da cigaba.
Shugaban Hukumar NDE, Mista Silas Agara ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da Shafin rajista ta yanar gizo a birnin Abuja, inda ya ce tsarin zai kasance cikin gaskiya da adalci, kuma an tsara shi ne domin bai wa kowane dan kasa dama ba tare da nuna bambanci ba. “Mun kammala mataki na farko cikin nasara, kuma mun samar da kayan aiki da cibiyoyi a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya don gudanar da wannan mataki na biyu cikin sauki,” in ji shi.
Agara ya ce duk wanda ke son shiga shirin zai bukaci lambar NIN da kuma shedar zama a cikin wata jiha ta Najeriya, ko da ba asalin can jihar yake ba. Ya bayyana cewa ’yan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 45 ne kadai za su iya yin rajista, kuma za su samu horo a fannoni sama da 30 na sana’o’in hannu da fasahar zamani, bisa bukatun tattalin arzikin kowace jiha. “Misali, abin da ke da amfani a Abia ba lallai ya dace da Adamawa ba, shi ya sa muka tsara horon bisa ga bukatun kowacce jiha,” in ji Agara.
An bude Shafin rajista ta yanar gizo kamar haka: www.nderegistrationportal.ng
Za a cigaba da rejista tun daga 28 ga Yuli zuwa 11 ga Agusta, 2025, yayin da za a fara tantance bayanan masu nema daga 12 zuwa 22 ga Agusta. Ya gargadi jama’a da su guji yaudarar masu karbar kudi ko amfani da hanyoyin da ba na hukuma ba. “Shirin kyauta ne gaba daya, kuma duk wani yunkuri na damfara, a gaggauta kai rahoton ga ofisoshin NDE na jihohi ko hedikwata,” in ji shi.