
01/07/2025
DA DUMI-DUMI: Zargin Yi wa Jam'iyyar Adawa Aiki, An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC na Nasarawa
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Hon. Aliyu Bello, an dakatar da shi daga jam’iyyar daga gunduman sa, sak**akon zargin goyon bayan wani ɗan takara daga wata jam’iyya daban.
Shugaban Gundumar Gayam, Ibrahim Ilyasu, ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Lafia, inda ya bayyana cewa dakatarwar ta zo ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, musamman a Sashe na 21 na dokan party. Ya ce Hon. Bello ya aikata babban laifi na nuna goyon baya ga abokin hamayyar jam’iyya, wanda hakan ya sabawa dokokin jam’iyyar.
“A matsayina na shugaban gunduma, tare da sahalewar sauran ‘yan kwamitin zartarwa, mun cimma matsaya bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, cewa daga yau, Hon. Aliyu Bello, an dakatar da kai daga jam’iyyar APC,” in ji Ilyasu.
Ilyasu ya kara da cewa akwai hujjoji da s**a tabbatar da cewa Bello yana taimakawa da kuma gudanar da yakin neman zabe ga wani ɗan takara daga wata jam’iyya daban, abin da kan iya janyo jam’iyyar APC cikin rikici da tabo.