19/09/2025
Rikicin ƙarin kuɗin makaranta: Prime College za ta maka gwamnatin Kano a kotu kan umarnin rufe makarantar
Makaranta mai zaman kan ta, Prime College Kano ta bayyana ƙin amincewarta kan matakin da Hukumar Kula da Makarantun Masu Zaman Kansu (PVIB), na ƙoƙarin rufe makarantar sak**akon sabani kan karin kuɗin makaranta.
A cikin wata sanarwa da lauyoyin makarantar, ƙarƙashin Aliant Qais Conrad Laureate su ka fitar a yau Juma’a, makarantar ta ce dole ne ta bayyana matsayinta bayan da aka kai mata umarnin kotu daga Wata Kotun Majistare a Kano, wacce ta umarrci ta janye karin kuɗin makarantar na shekarar karatu ta 2025/26.
A watan Yuli 2025, Prime College ta sanar da karin kuɗin makaranta na shekarar karatu mai zuwa, tana mai cewa hauhawar farashi da buƙatar kiyaye ingancin koyarwa da gine-gine ne s**a sa hakan.
Hukumar makarantar ta bayyana cewa, sun ba da sassaucin biyan kuɗi ga iyaye, tare da tabbatar da cewa babu ɗalibin da za a hana karatu saboda kasa biyan kuɗin makaranta
A cewar makarantar, fiye da kashi 94% na iyaye sun biya sabon farashin, amma ƙasa da iyaye 20 ne s**a ƙi, inda su ka kai ƙara ga PVIB don ta shiga tsakani.
Sanarwar ta ce Shugaban hukumar ta PVIB, Malam Baba Abubakar Umar, ya kai ziyara makarantar tare da su waɗannan iyaye da su ka yi tutsu, inda ya kafa wani kwamitin gaggawa na iyaye daga cikin mambobin PTA da ya ƙunshi iyaye 8 da malamai 5.
Sanarwar ta kara da cewa kwamitin ya kada ƙuri'a a goyon bayan karin kuɗin, amma daga bisani PVIB ta ce zaman bai yi daidai ba, sannan ta bayar da umarnin a gaggauta janye karin kuɗin.
Hukumar makarantar ta yi zargin cewa ƙoƙarin tuntubar shugabannin PVIB ya gamu da "cin mutunci da kuma kunyatr wasu a bainar jama’a."
A ranar Laraba, 17 ga Satumba, makarantar ta samu umarnin kotu daga wata Kotun Majistare a Kano, wanda ke hana ta aiwatar da sabon karin kuɗin da kuma dakatar da ayyukan makarantar.
Prime College ta ce tana nazarin daukar matakin doka domin samun adalci a kotu, inda ta sake jaddada cewa tana aiki bisa ka’ida, tana mai gargadi cewa dakatar da ilimin yaran da ba su da laifi zalunci ne.
“Bai dace ba a dakatar da karatun yaran da ba su da laifi, ko da na rana guda ne — b***e na makonni — ba tare da sauraron ɓangarenmu na magana ba,” sanarwar ta ƙara da cewa.