26/07/2025
Fassarar Jawabin Sanata Henry Seriake Dickson A Zaman Majalisar Dattawa Na Musamman Kan Jimamin Rasuwar Buhari
Suna na Sanata Henry Seriake Dickson daga Bayelsa ta Yamma. Ina godiya ga Shugaban Majalisar Dattawa kan wannan damar da ka bani ta cewa abu daya ko biyu kan tsohon Shugaban Kasa marigayi Muhammadu Buhari.
Idan na duba a wannan zauren majalisar ni kadai ne Gwamnan da ke a jam'iyyar adawa a lokacin da aka zabi Buhari a matsayin Shugaban Kasa a 2015 don haka daidai ne wannan damar da ka bani ta magana a kan sa.
A madadin al'ummar Bayelsa ta Yamma mun shiga cikin shugabannin majalisa da Shugaban Kasa, al'ummar masarautar Daura da al'ummar Nijeriya bakidaya wajen jajantawar wannan babban rashin maras misaltuwa da muka yi. Zan je masarautar Daura wadda nake neman sarauta domin jajantawa mai girma Sarki.
'Yan Nijeriya kalilan ne ubangiji ya baiwa irin dama da sukunin da Buhari ya samu, na farko a matsayin shugaban mulkin soji da karancin shekaru na biyu a matsayin zababben shugaban kasa a wa'adin mulki biyu, kuma ya kammala ya yi ritaya a gida.
Kasar mu ta na cikin jimami, ina son in shiga cikin wannan majalisar da al'ummar kasa wajen yabawa Shugaban Kasa wanda ya jagoranci Gwamnatin Tarayya wajen shirya jana'izar musamman ta gwamnati wadda irinta ya kamata a rika yi wa shugabannin mu.
Na bayyana hakan ne domin tsohon Shugaban Kasa, Shehu Shagari bai samu irin wannan karramawar ba don haka na yadda da abin da Tinubu ya yi abin yabawa ne wanda ya kamata a bayyana a matsayin abin da ya kamata a yi wa shugabannin mu da s**a yi kokari wajen bautawa kasa.
Za mu iya kin yadda da manufofinsu da ma siyasarsu saboda bambancin ra'ayin siyasa amma mu mutunta jagorancin da s**a yi, don haka Tinubu ya yi abin da ya kamata ya zama abin koyi.
Shugaban Majalisa, ba shakka Buhari ya gudanar da rayuwar hidimtawa kasa, za mu iya kin yadda da manufofinsa domin ni kaina ban yadda da yawa daga cikin manufofinsa ba.
A yayin da aka cire babban mai shari'a na kasa Walter Onnoghen a wani yanayi, na tara Gwamnonin Kudu- Maso- Kudu muka dauki matsaya daya kuma Buhari bai dauki wani mataki kan mu ba ko ni kaina da na jagorance su.
Ban yadda da Buhari ba kan batun da ya gabatar na kashi uku na al'ummar da ke da albarkarun mai maimakon kashi biyar da muka bukata.
Haka ma ban yadda da matakinsa ba lokacin da shi da Gwamnan Babban Bankin Kasa, Godwin Emefele s**a yi abin da s**a yi wajen canza kudade.
Bugu da kari ban kuma goyi bayyansa ba a bisa kasa shirya taron canza fasalin kasa amma duk da haka Buhari a dukkanin tarukan mu yana nuna dabi'a tagari duk da girman matsayinsa da bambancin shekaru amma yana girmama dukkanin mu Gwamnonin jam'iyyar adawa tare da mutunta mu.
Baya ga wannan a kodayaushe yana yi mana uzuri, zan bada misali da lokacin da ya karbi mulkin kasa a 2015 kuma tattalin arzikin kasa ya tabarbare zai iya yin siyasa da yanayin ta hanyar bayar da tallafi ga Gwamnonin jihohin da jam'iyyarsa ta APC kawai ke mulki kamar yadda aka matsa masa amma bai yi hakan ba sai ya bayar da tallafin ga dukkanin Gwamnoni bakidaya.
Ina ganin dayan Gwamnan da ke nan a lokacin shine Adams Oshomhole, Buhari ya tabbatar dukkanin Gwamnonin jihohi abin da ya kamata a baiwa jihohi an ba su, bai nuna bambancin wannan jihar ta PDP ce ko ta APC mai mulki ba.
Da yawa 'yan Nijeriya ba su san irin matsin tattalin arziki da kasa ta shiga ba a 2015 har zuwa 2020 lokacin da abubuwa s**a daidaita ba, a lokacin Buhari da mataimakinsa Osinbajo da tawagar da yake jagoranta ta masana tattalin arziki s**a fito da hanyoyin samun kudi da goyon bayan majalisar dokoki ta kasa domin tallafawa jihohi wanda ba don hakan ba da kasa ta tabarbare, don haka ya zama wajibi mu gode masa.
Haka ma a yayin da na nemi wa'adin mulki na biyu a 2015, Buhari ya kira ni ya ce mani Dickson kar ka damu na kira hukumar zabe da shugaban sojoji da shugaban jami'an tsaron farin kaya na DSS na ba su umurnin su fadawa jami'ansu su yi abin da ya kamata, ya kuma sake kira na ya ce sako ya isa, ka je ka fara yekuwar neman zabe.
Buhari ya ce mani ya fuskanci magudin zabe a kasar nan don haka a matsayinsa na shugaban kasa ba zai yadda ya hanawa al'umma abin da s**a zaba ba, na yi masa godiya.
Zabe na shine zabe mafi zafi da aka yi a kasar nan wanda ban tunanin an taba yin irinsa, duk da ba su yi biyayya ba, ina da tabbacin shugaban kasa ta, ya bada umurnin duk da yake ba su bi umurninsa ba amma an yi zabe na kuma yi nasara.
A lokacin da muke a kotun koli a 2020 bayan kammala wa'adina, Buhari wanda mutanensa suke a Bayelsa domin rantsar da dan takarar APC wanda aka bayyana ya samu nasara a zaben, amma bai kira kotun koli domin a yi watsi da karar mu ba har kasa da awanni 24 a inda kotun ta yanke hukuncin dan takarar su bai cancanta ba amma Buhari ya karbi hukuncin.
A lokacin da ya hadu da Gwamnan, sai cikin barkwanci ya ce masa wato kai da maigidan ka ku ke da fannin shari'a (s**a yi dariya) wannan dabi'ar mutanen kwarai ce.
Daga karshe muna yabawa iyalansa kan samun shi da muka yi a wannan kasa, muna rokon Allah ya gafarta masa ya yafe masa kura- kuransa.
Jamilu Abubakar.
Mataimaki na musamman kan yada labarai ga Sanata Henry Seriake Dickson.
26/07/2025.