06/11/2025
Zaman Juyayin Shahadar Sayyada Zahra (S.A) A Abuja.
Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), ta gudanar da zaman juyayin shahadar 'yar Manzon Allah (S.W.W) Sayyada Zahra (S.A) zama na karshe a Abuja.
Rana ta uku wanda shine ya zama Rana ta karshe (Khatama) na zaman juyayin da Harkar Musuluncin ta gabatar, a Rana ta karshen an gudanar da wakokin juyayi na shahadar Sayyada Zahra (S)" sannan aka gudanar da Tamsiliya daga 'yan IM Production, daga bisani, aka gabatar da mai wajabi kamar yadda aka saba, Sayyid Badamasi Tambuwal, yayi jawabi akan Shahadar Sayyada Zahra (S), sannan aka rufe Taron da addu'a.
Allah ya kara ninka azabarsa ga makasan 'yar Manzon Allah (S), Assalamu alaiki ya Zahra 😢
I-M Charis
AliSajjad Ibn Taheer
6th/ Nov/ 2025