23/01/2025
ALLAH YA SA HALIN DA MUKE CIKI A KASAR NAN YA ZAMA KAMAR NA "MATAR NAN TA LOKACIN ANNABI DÃWUD (AS)"
حَدِّثُوا عن بَنِي إِسْرائِيلَ وَلا حَرَجَ
أخرجه أبو داود (٣٦٦٢)، وأحمد (١٠١٣٤)
Akwai wata mata a lokacin Annabi Dãwud (AS) da ta shiga gurinsa cikin fushi; ta ce da shi: "Ya Annabi Allah! Shin Ubangijinka azzalimi ne ko mai adalci ne? Sai ya ce da ita: "Ubangijina mai adalci ne. Me ya faru? Sai ta ce: "Ni bazawara ce da nake da yara marayu, kanana, ba ni da komai, kuma babu wanda yake taimaka min. Ina rufawa kaina da iyalina asiri ne ta hanyar sanã'ar sãka da nake yi. Yau na yi sãka ta kalar ja, na tafi kasuwa zan siyar, kawai sai wani Hankaka ya zo ya dauke min sãkar, ya tafi da ita. kuma ita ce jãri na baki daya. Yanzu ya zan yi. Adalcin ke nan?
Sai Annabi Dãwud (AS) ya ce da ta: "Allah yana da hikima; kuma duk abin da kika ga ya yi, to akwai hikima da adalci a ciki... Amma nawa ne kudin sãkar taki baki daya? Sai ta ce Dinare daya,..
Suna cikin tattaunawa, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo gurin Annabi Dãwud (AS) s**a ce: "Ya Annabin Allah! Yau mun ga abin mamaki. Muna cikin jirgin ruwa; a tsakiyar kogi, sai jirgin namu ya būle,.. mu dab da halaka, sai muka yi bakance 'idan Allah ya ceratar da mu, kowannen mu zai yi sadaka da Dinãre 100.' Kwasam! Sai wani Hankaka ya jefo mana wata sãka ja, sai muka toshe bular da ita,.. Allah ya kubutar da mu. Saboda haka, ga Dinãre 1000 nan ka sanya shi yadda ka ga ya dace.
Sai Annabi Dãwud (AS) ya juyo gurin wannan mata ya ce da ita: "Kin ga hikimar Allah da adalcinsa ko? Dauke wannan Dinãre 1000 [ninkin kudin sakarta sau 100] duk naki ne.
YA ALLAH KA WARWARE MANA KUNCI DA TALAUCI DA RASHIN TSARO DA MUKE FAMA DA SHI A KASAR NAN TA MU
F0ll0w me the wireless Java, c,&app development