
15/06/2025
Saura kiris Iran ta mayar da Isra'ila kufai – Mejo Amir.
Sabon kwamandan rundunar sojin, Janar Mejo Amir Hatami, ya bayyana shirye-shiryen sojojin Iran na kai mummunan hari ga gwamnatin Isra'ila.
A cikin saƙon da ya aikawa Jagoran Juyin Juya Hali na Musulunci, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a ranar Lahadi, Janar Hatami ya gode masa bisa amincewa da naɗa shi a matsayin sabon shugaban sojojin ƙasa.
Yayin da yake sabunta mubaya’a ga manufofin juyin juya halin Musulunci, sabon kwamandan ya ce sojojin Iran daga sassa daban-daban — Rundunar ƙasa, Rundunar Sama, Rundunar Ruwa da Rundunar Kariya ta Iska — za su kare 'yancin kai da mutuncin iyakokin ƙasar Iran da kafa gwamnatin Jamhuriyar Musulunci da gaskiya da ƙwazo da rikon Amana..
Janar Hatami ya jaddada rawar da rundunar soji ta taka wajen kare ƙasar nan take bayan harin da gwamnatin Isra’ila ta kai a farkon safiyar ranar Juma’a, yana mai cewa rundunonin sojin za su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin rusa gwamnatin Isra'ila da yaudarar duniya wacce ke kashe yara.
Gwamnatin Isra’ila ta kai hari a wasu unguwannin zama a Tehran da kuma wuraren soja da makamashi na nukiliya a wasu sassan ƙasar Iran a safiyar ranar 13 ga Yuni.
A cikin harin, an kashe manyan hafsoshin soja da masana nukiliya akalla shida, tare da fararen hula da dama.
Rundunar Sojin Iran ta mayar da martani da gagarumin luguden makamai masu linzami a wasu birane da ke yankunan da Isra’ila ta mamaye.