25/04/2026
USTĀZIYAH 🥰🥀
Idan har ba ka auri Ustāziyah ba, to ba ka more wa aure ba
Sadaukarwa zuwa ga sisters (Ustazai)
Idan aka ce Ustāziyah, ana nufin mace Tagari mai addini, irin wadda Annabi ﷺ ya ce
وَعَلَيْكَ بِذَاتِ الدِّينِ تَرِبَتْ يَدَاكَ.
Ma’ana
Ka zaɓi mace mai addini, hannayenka su yi albarka.
Wato
idan kana so ka ji daɗin aure, ka more shi, to ka auri Ustāziyah
Shi ya sa a hadisai da s**a zo game da morewar duniya, mafi alheri cikinsu shi ne auren mace ta gari. Za ka same su sun zo da riwayoyi masu yawa domin ka gane cewa abu ne babba.
A riwayar Muslim
Daga Abdullāhi ɗan Amr bn al-ʿĀṣ (RA)
الدُّنْيَا مَتَاعٌ وَخَيْرُ مَتَاعِهَا الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ.
Ma’ana
Duniya abin morewa ce, mafi alherin abin morewarta kuwa ita ce mace ta gari.
A riwayar Ibn Mājah
إِنَّمَا الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَلَيْسَ مِنْ مَتَاعِ الدُّنْيَا شَيْءٌ أَفْضَلُ مِنَ الْمَرْأَةِ الصَّالِحَةِ.
Ma’ana
Duniya dai abin morewa ce, kuma babu wani abu daga cikin morewarta da ya fi mace ta gari
Duniya wurin jin daɗi ce, amma babu wani abu daga cikin jin daɗin duniya da ya fi ka samu mace ta gari.
A wata riwaya
مَا اسْتَفَادَ الْمُؤْمِنُ بَعْدَ تَقْوَى اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ خَيْرًا لَهُ مِنْ زَوْجَةٍ صَالِحَةٍ.
Ma’ana
Mumini bai samu wata fa’ida mafi alheri ba bayan tsoron Allah face mace ta gari.
A riwayar Ṭabarānī (a cikin al-Awsaṭ):
Daga Anas (RA)
مَنْ رَزَقَهُ اللَّهُ امْرَأَةً صَالِحَةً، فَقَدْ أَعَانَهُ عَلَى شَطْرِ دِينِهِ، فَلْيَتَّقِ اللَّهَ فِي الشَّطْرِ الْبَاقِي.
Ma’ana
Duk wanda Allah Ya ba shi mace ta gari, to Ya taimaka masa a rabin addininsa, sai ya ji tsoron Allah a rabin da ya rage.
A wata riwaya daga Ibn ʿAbbās (RA)
Manzon Allah ﷺ ya ce:
أَرْبَعٌ مَنْ أُعْطِيَهُنَّ فَقَدْ أُعْطِيَ خَيْرَيِ الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ:
قَلْبًا شَاكِرًا، وَلِسَانًا ذَاكِرًا، وَبَدَنًا عَلَى الْبَلَاءِ صَابِرًا، وَزَوْجَةً لَا تَبْغِيهِ حُوبًا فِي نَفْسِهَا وَلَا مَالِهِ
Ma’ana
Abubuwa huɗu, duk wanda aka ba shi su, to an ba shi alherin duniya da lahira: zuciya mai godiya, harshe mai ambaton